1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da gaske Merkel ta ke game da hadin kan Turai

June 8, 2012

A dangane da rikicin bashi da yayi wa ƙasashen Turai katutu, shugabar gwamnatin Jamus ta yi kira da ƙarfafa haɗin kan siyasa a Turai.Peter Stützle ya rubuta sharhi

https://p.dw.com/p/15B4Q
Hoto: Reuters

Sai dai kawo yanzu da yawa daga cikin al'ummomin nahiyar na saka ayar tambaya game da kyakkyawar aniyar Merkel ɗin ga nahiyar Turai. Hakan kuwa ba daidai ba ne, inji Peter Stützle a cikin wannan sharhi.

Abubuwa a bayyane suke ga tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl. Kasancewa ya tashi ne a yankin kan iyakar Jamus da Faransa, kuma tun yana matashi musamman bayan yaƙin duniya na biyu, da shi da abokansa sun yi ta buge shingen da ya raba kan iyakokin ƙasashen biyu. Daga bisani bayan ya zama ɗan siyasa ya yi ta bayyana haɗin kan Jamus da haɗin kan Turai tamkar fuskoki biyu na ƙwandala. Kohl ya kasance mai ƙaunar nahiyar Turai a zuci. A saboda haka a shekarar 1998 shugabannin ƙasashen tarayyar Turai suka girmama shi da sunan gwarzon Turai.

Ita ma Angela Merkel ta yi ta magana game da fuskoki biyu na ƙwandala, sai dai ba bu zahirin haka a gare ta. Ita dai ta tashi ne a tsohuwar ƙasar Jamus ta Gabas, wadda al'umominta suka riƙa ganin Jamus ta Yamma ta tsallaken katanga, ba tare da hangen biranen Paris ko Roma ba. Amma a lokacin da guguwar sauyi ta kaɗa sun nuna cewa Jamus ƙasa ɗaya ce al'umma ɗaya.

Helmut Kohl auf der Frankfurter Buchmesse 2010
Helmut Kohl gwarzon TuraiHoto: AP

Sai dai wannan ɗokin na haɗewar Jamus, in banda ga wasu ɗaiɗaikun ƙungiyoyi, ba abu ne na matsanancin ra'ayin kishin ƙasa ba. Babu inda aka ta da tutocin Turai da ƙawayata motoci da sitikar Turai da ya kai Jamus. Tun da farkon fari batun Turai ya zama wani ɓangare na haɗin kan Jamus. Ga wasu ƙalilan hakan ya bayyana fili fiye ga Angela Merkel wadda daga bisani ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Helmut Kohl.

Merkel ta san cewa Jamus na buƙatar Turai

Masu kishin nahiyar Turai wanda tsohon shugaban gwamnatin Jamus Konrad Adenauer ke cikinsu, tun bayan yaƙin duniya na ɗaya suka bayyana haɗin kan Turai tamkar wani batu na yaƙi da kuma zaman lafiya, kuma sun yi gaskiya. Helmut Kohl ya ga yaƙin duniya na biyu saboda haka ya yi ta magana da babbar murya game da haɗin kan Turai a matsayin wani gagarumin aikin zaman lafiya. Ita ma Angela Merkel ta bayyana wannan tunanin a cikin jawabai da yawa. Ko da yake ba da ƙarfi ba, amma hakan ba ya nufin tana ɗari ɗari da batun.

Deutschland Helmut Kohl und Angela Merkel
Hoto: AP

Baya ga Kohl, sauran masu ƙaunar Turai a zuci a nan Jamus kamar Wolfgang Schäuble suna da ƙwararan dalilan yin haka. Sun yi amanna cewa Jamus mafi yawan ƙasashe maƙwabta a Turai, a cikin wata haɗaɗɗiyar nahiyar Turai za ta iya samun kyakkyawar makoma a fannonin siyasa da tattalin arziki. Ita ma Angela Merkel tana da wannan ra'ayi. Domin ta gane cewa zaman tare a Turai na cikin haɗari sakamakon rikicin bashi, a saboda haka take daɗa yin kira da a ƙara samun haɗin kai tsakani.

Mawallafa: Peter Stützle / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi