1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Hukumar UNESCO ta karɓi wakilcin yankin Palasɗinu

November 1, 2011

Duk da mummunar adawa daga Amerika, amma yankin Palasɗinu ya sami karɓuwa, tare da cikakken wakilci a hukumar ilimi, kimiyya da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNESCO, tare da goyon bayan kasashe 107.

https://p.dw.com/p/132xh
Taro UNESCO na 36 a Paris da wakilcin PalasdinuHoto: dapd

Kasashe 107 ne suka amince da daukar wannan mataki, lokacin babban taron da hukumar tayi a Paris, yayin da kasashe 14 suka yi adawa, wasu 52 kuma suka yi rowar kuri'un su. Hakan ya kai ga tambayar, shin wannan nasara ana iya daukar ta a a matsayin matakin farko kan hanyar Palesdinu na kasancewa yantacciyar kasa?

Ga Palesdinawa, karbar su da aka yi a hukumar UNESCO babu shakka wata nasarace ta farko, kan hanyar kasancewar sun sami cikakken wakilci a majalisar dinkin duniya. Kudirin da hukumar ilimi, kimiyya da al'adu ta majalisar dinkin duniya ta dauka, ana iya fahimtar sa a matsayin wata alamar dake nuna cewar a karshe dai majalisar ta dinkin duniya a shirye take ta taimakawa Palesdinawan ya zuwa ga samun yantacciyar kasar kansu.

Palästina Aufnahme UNESCO Riad al-Maliki Elias Sanbar
Ministan harkokin wajen Palasdinu Riad al-Maliki(hagu) a zauren taron UNESCOHoto: dapd

Bugu da kari kuma, wannan amincewa da suka samu a hukumar UNESCO mataki ne da zai zama goyon baya ga wannan kokari nasu, saboda a yankin da aka dade ana fama da rikici a cikinsa na Israila da Palesdina, inda kasashen yamma sukan so kwatanta shi a matsayin yanki mai tsarki, cike yake da abubuwan tarihi da sanannun kayaiyaki na al'adu da ake takaddama kansu tsakanin bangarorin biyu. Tsohon birnin Kudus misali, dake dauke da gine-gine na addini, wanda kuma birnine da Israila ta mamaye shi ta hanyoyi na haramun, ko kuma wurare da dama da Israila ta mamaye masu dauke da kayaiyakin tarihi na karkashin kasa, wadanda gaba daya wadanda kayaiyakin da zaran an hako su, sukan kare a gidajen ajiye kayan tarihi na Israila, ko kuma kogin Dead Sea, da kasashen Israila da Jordan da Palesdinawa duka suke daukar sa da muhimmanci kuma suke matsa lambar a amincedashi a matsdayin wurin da UNESCO ta amince da kasancewar sa na tarihi. Ya zuwa yanzu Palesdinawa basu da wata hanya ta cin gajiyar wnanan kogi, musamman basu da damar amfana daga albarkatun gishiri ko sauran ma'adinai da kogin yake dasu. Dangane da haka, wakilcin Palesdinu a hukumar ta UNESCO yana iya bata damar karin fadi aji a matakan kare kogin.

Ana kuma iya daukar wakilcin da Palesdinun ta samu yanzu a UNESCO a matsayin wata nasara ta farko, da ba zata taimakawa Palesdinun kan hanyar cimma burin wannan yanki, wato samun yantacciyar kasa da zata zauna kafada da kafada da Israila ba, musamman saboda kasashen dake da muhimmanci a neman cimma wnanan buri na Palesdinawan, sunce ba zasu bada goyon bayan su ba. Daga cikin wadannan kasashe har da Amerika, kasar da a yanzu ma tace zata dakatar da gudummuwar kudadenda ta saba baiwa hukumar ta UNESCO. Haka nan ita ma Jamus ta kada kuri'ar adawa da daukarPalesdinu a hukumar, saboda wai wannan mataki yana iya haddasa cikas a kokarin sake komawa kan teburin shawarwari tsakanin Israila da Palesdinawa. Bugu da kari kuma, wai ba'a bukatar kawo cikas a tattaunawar da ake yi yanzu a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, game da karbar Palesdinu a majalisar.

Frankreich Gebäude in Paris Unesco droht Austritt der USA Palästinenser aufgenommen
Tarihi kan Palasdinu a hedikwatar UNESCO a birnin ParisHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai wadannan bayanai ne da basu zama masu gamsarwa ba. Shawarwari da Palesdinawa da Israila suka fara a yan kwanakin baya, wadanda ma ba shawarwari jne na kai tsaye ba, amma sai ta hannun wakilan masu shiga tsakanin, wato Rasha, majalisar dinkin duniya, Amerika da kungiyar hadin kan Turai, tuni suka rushe saboda Israila taki dakatar da manufofin ta na ci gaba da gina matsugunan Yahudawa a yankunan da ta mamaye, ta kuma ki karbar yiwuwar mutunta iyakokin yantacciyar kasar Palesdin idan ta samu. A game da batun karbar kasar Palesdinu a majalisar dinkin duniya, tuni gwamnatin ta Jamus ma ta yanke kudirin ta: tace zata yi adawa da haka, duk kuwa da shekaru da tayi tana fada da fatar baka cewar tana goyon bayan samun kasar Palesdinu kusa da Israila.

Daidai ne, kuma ya dace da UNESCO ta karbi Palesdinu a matsayin cikakkiyar wakiliya a cikin ta. Rashin yin haka, zai zama rashin hangen nesa ne a fannin siyasa daga hukumar.

Mawallafi: Bettina Marx/ Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman