Yanayin dai na zama irin wanda wasu fitattun shugabannin gwamnati suka samu kansu a shekarun 1949 da shekarun 1982 zuwa 1998, wato Konrad Adenauer da Helmut Kohl. Sai dai har yanzu Angela Merkel na rike da ragamar jam'iyyarta, kuma yanzu ta zabo sabbin jini da take son sakawa cikin majalisar ministoci. In har batun kafa gwamnatin hadaka da 'yan adawa ya tabbata, haka kuma sabuwar sakatariyar jam'iyyar CDU da a ka nada ma kamar ministocin da Merkel ta zaba, na zama wata matashiya idan a ka kwatanta da shekarun Merkel kamar yadda Christoph Strack na DW ya rubuta a wannan sharhin.
Watanni biyar bayan gudanar da zabe, amma har yanzu jam'iyyar Merkel na zawarcin 'yan jam'iyyar don kafa gwamnatin hadaka da wasu jam'iyyu, kuma bisa gagarumin rinjaye 'yan jami'yyarta suka amince da yin gwamnatin hadakar. Wato dai a ci gaba da yadda a ke mulki kamar da. To sai dai ga mahalarta taron jam'iyyarta a wannan karon ba wai komai zai dore kamar da ba.
Merkel ba ta kasance tauraruwar jam'iyya ba
Taron wuni guda da jam'iyyar ta gudanar za a iya cewa ba wai taron da za'abi abin da Merkel ke so ne ba. Gabanin fara taron shugabar gwamnatin ta yi dogon jawabin na lallashin 'yan jam'iyyar su amince da kafa gwamnatin hadaka, sa'o'i hudu bayan haka Annegret Kramp-Karrenbauer, ta yi wani dogon jawabi mai kada hankali, tamkar yadda ake son sakatare janar na jam'iyya ya yi, a lokacin da jam'iyya ta shiga mayuwacin hali.
Merkel ta nemi wakilai kimanin dubu daya da su amince a kafa gwamnatin hadaka da babbar jam'iyyar adawa ta SPD, inda kuma akasarin wakilai suka amince. A duk tsawon jawabin na Merkel na kusan sa'a guda, bata ambaci ko wace jam'iyya ba, sai dai ta tabo batun jam'iyyar mai kyamar baki ta AfD, wace gabanin zabe, Merkel kusan bata taba ambata ba. Inda Merkel ta soki tsarin AfD mai kyamar Yahudawa, tamkar yadda wasu masu tsattsauran ra'ayi kasar ta Jamus ke yi.
Daga nan ne fa 'yan jam'iyyar suka fara nuna fusatarsu da yin kaito bisa jagorancin Merkel, inda wasunsu suka yi ta jefa kalamai marasa dadi, wasu suka bayyana ra'ayinsu cewa basu yarda a yi gwamnatin hadaka ba.Taron na CDU da ya gudana Litinin, ya kasance daya daga cikin tarukan da a ka taba samun hargizi da fusata, inda a ka yi mahawarori masu zafi na sukar shugabannin jam'iyya. Ga tsofaffin 'yan fansho kuwa suna gode wa Merkel, yayin da sabbin jini kuma ke sukar sabbin tsare-tsaren jam'iyyar kamar yadda a ka ji daga bakin sabuwar sakatariyar jam'iyyar. A bisa sakamakon zaben kasar na bara da aka samu, hakan ya bude mahawarori masu karfi, inda a ke ta yin suka wanda kuma ya bayyana baraka da ke cikin jam'iyyar ta Angela Merkel.
Kyakkyawan fata ga ma'aikata
Bayan jawabin da aka ji a babban taron jam'iyyar CDU, kusan babu wani kyakkyawanrfata ga ma'aiakata, bayan da Merkel ta ambaci wasu ministoci, wasu daga cikin wakilan sun yi ta tafa mata har na kusan mintuna hudu, wasu kuwa ko daga hannunsu basu yi ba. Taron da ya guduana a Berlin ya jawo sukar da ba'a zaci ji daga wakilai ba. A yanzu dai abin jira shi ne taron jam'iyyar SPD, inda za su kada kuri'ar kafa gwamnati tare da Merkel ko a'a. Kafin nan dai Angela Merkel da sabuwar sakatariyar jam'iyyar CDU su ne za su ci gaba da hada woyoyin da za su ceci makomar jam'iyyar ta CDU da ta samu mummunan koma baya a zaben da ya gabata.