Sharhi: Kotun kare tsarin mulki yace dokar ceto Euro bata keta tsarin mulki ba
September 7, 2011A lokacin yanke hukuncin sa, kotun ya karfafa matsayin majalisar dokoki a matakan da gwamnatin take dauka. Manyan alkalan na taraiya sun dauki matakin da ake iya kwatanta shi a matsayin kwarewa a aiyukan su. Hukuncin da suka zartas ya kara karfafa matsayin majalisar dokokin taraiya dake neman rasa muhimmancin ta, tattare da matakan ceto kudin na Turai wato Euro, amma a lokaci guda, hukuncin nasu bai kawo wani hadari ko barazana ga kokarin da gwamnati take yi na ceto Euro ba.
Inda alkalan sun so, da sun yi watsi gaba daya da dokar da ta shafi daukar manufofin tabbatar da hana fadi-tashin kudin Euro, wadda a karkashin dokar Jamus take daukar matakan ceto kasashen da matsalar ta kudin na Euro ya shiga ta jefa su ciikin mummunan matsalar bashi. A karkashin wannan doka, majalisar dokokin Jamus, wato Bundestag ta rasa karfin fadi aji a al'amuran kudi na kasar, wanda bisa bisa manufa, alhakin ta ne ta kula dashi, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar. Tsarin mulkin na Jamus ya tanadi cewar batun kasafin kudi, ko al'amuran kudi na kasa baki daya, al'amari ne dake karkashin ikon majalisar dokokin ta taraiya. A daura da haka, a dokar da ta shafi daukar matakan ceto kudin Euro, gwmanatin taraiya an nemi tayi kokarin samun amincewar kwamitin kasafin kudi na majalisar dokoki ne kawai, amma ba a tattauna majalisar ba, kafin gwmnatin ta amince da bada taimako ga kasashen da rikicin kudin na Euro ya jefa su cikin bashi.
Bisa manufa, wannan mataki na gwamnati ya sabawa tsarin mulkin Jamus. To sai dai inda kotun kololuwar ta Jamus a sakamakon hakan ta soke wannan doka gaba daya, da hakan ya kawo hadari ga matakan da tuni aka fara dauka na hana rushewar kudin Euro gaba daya. Inda hakan ya faru da kuwa sakamakon da za'a samu zai zama mai muni matuka. Saboda haka ne manyan alkalan suka juya ga wata dabara, inda suka ce dokar ceto kudin na Euro bata sabawa tsarin mulki ba, amma suka nemi gwmanatin tayi wa dokar gyara, yadda majalisar dokoki zata rika samun damar fadi aji a duk abin da ya shafi kudin na Euro, wato a takaice, alkalan suka ce nan gaba idan ba tare da amincewar kwamitin kasafin kudi na majalisar dokoki ba, gwmanati kada ta sake daukar wani mataki na ceto Euro.
Ana iya cewa hukuncin da kotun na kare tsarin mulkin taraiya ya gabatar, ya zo a daidai lokacin da ya dace, domin kuwa ranar Alhamis, majalisar dokoki ta Bundestag take tattaunawa a game da dokar da zata baiwa majalisar damar tofa albarkacin bakin ta a game da duk wani mataki da gwmanati zata dauka nan gaba na ceto Euro. Majalisar ta bukaci wannan doka ne, saboda tsoron da yan majalisar suke nunawa cewar sun fara rasa muhimmancin su a al'amuran da gwamnati take tafiyarwa. Saboda haka ne alkalan kotun suka karfafawa yan majalisar matsayin su da kokarin kawar da wannan tsoro dake zukatan su. A lokaci guda kuma, manyan alkalan sun dauki matakin hana kewaye majalisar dokokin nan gaba a al'amuran gwamnati. Saboda haka ne ake iya cewar hukuncin da alkalan suka gabatar, wata babbar nasara ce ga democradiya.
Mawallafi: Peter Stützle/Umaru Aliyu
Usman Shehu Usman