Nazari a game da yunkurin juyin mulkin Gabon
January 8, 2019Sai dai al'amarin na neman zama ruwan dare ne karkashin mulkin Ali Bongo saboda so biyu gwamnatinsa na fuskantar juyin mulkin da suka ci tira a 2009 da 2019. Hasali ma da taimakon bayanan sirri da Faransa ta saba bai wa magabata a Liberville ne ake amfani wajen murkushe duk wani yunkuri na hambarar da gwamnati. A fili take cewar tsohuwar uwargijiyar Gabon watau Faransa na goyon bayan mulkin sai Mahdi ka ture da iyalin Bongo suka shafe shekaru fiye da 50 suna yi a Gabon.
Kelly Ondo Obiang ya yi kasada wajen shirya juyin mulkin ba tare da samun goyon baya ba
Tabbas Laftana Kelly Ondo Obiang ba shi da kwarewa da goyon baya da za su bashi damar samun nasara, amma kuma a cikin jawabinsa na karbe iko ya susa wa al'umma inda ya ke yi musu kaikayi. Ya nunar da cewar gwamnatin da ke ciki haramtacecciya ce, saboda haka ne ya dauki wannan mataki ne domin ceto Gabon daga halin da take ciki. Sanin kowa ne cewar shugaba Ali Bongo ya shafe watanni uku a kasashen ketare sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, ba tare da an kafa gwamnatin rikon kwarya ba. Maimakon shugabar kotun tsarin mulkin Gabon Madeleine Mborantsua gwamnatin ta karya gaba ta hanyar kirkiro da wata sabuwar doka domin danka rikon kasar ga mataimakin shugaban kasa da kuma firaministan kasar. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa bangaren adawa kin sukar yunkurin juyin na mulki.Tun farko jam'iyyun adawa 44 sun yi kira da murya guda da aka kafa gwamnatin rikon kwarya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, amma jami'a a Libreville suka yi kunnen uwar shegu da wannan bukata.
Gwamnatin Gabon ba ta fito fili ba ta yi bayani dala-dala ba a game da abin da ya faru
A bangaren mulki kuwa sun shuru tamkar an shuka dusa babu wani na hannun damar Ali Bongo da ke kurin murkushe yunkurin na juyin mulki in banda kakakin gwamnati Guy-Bertrand Mapangou. Wannan ba ya rasa nasaba da gabar da ke tsakanin bangaro biyu da ke neman kakkange madafan iko idan Ali Bongo ya sauka ko kuma ta Allah ta kasance. Uwargidan shugaban kasa Sylvia ba ta jituwa da dan uwan shugaban wata Frederic Bongo da ke jagorantar wata runduna ta musamman. Har yanzu ba a san ko yana da masaniya dangane da yunkurin juyin mulkin ba ko akasin haka.