Sharhi: Rikicin siyasar kasar Yemen
December 6, 2017Tun da dadewa ba a juyayin mutuwa a kasar Yemen, inda tun shekaru biyu da rabi wani kawancen kasa da kasa karkashin jagorancin Saudiyya ke yakar 'yan tawayen Houthi a wani yaki da ya fi shafar al'ummar farar hular kasar, inda alkalumma suka ce wadanda suka mutu sakamakon yakin ya haura mutum dubu 10. Yanzu yakin ya rutsa da daya daga cikin madugan yakin wato Ali Abdullah Saleh da ya kasance shugaban kasar har zuwa shekarar 2012.
A ranar Litinin 'yan tawayen Houthi da ya kulla kawance da su watanni baya, suka halaka shi. A karshen makon jiya Saleh ya ce zai sauya sheka. Da hakan ya tabbatar da watakila kallon da ake masa na zama dan siyasa mai sassaucin ra'ayi da ke iya dasawa da duk wanda ya zai biya masa bukata. Mutuwarsa ba ta sa a dakatar da yakin a Yemen ba, maimakon haka ma dakarunsa ne ake sa rai za su raba gari da 'yan Houthi su kuma kulla kawance da bangaren mutumin ya gaje shi wato Shugaba Abed Rabbo Mansur Hadi, su yaki 'yan Houthi.
Duk wadannan abubuwa da ke faruwa a Yemen ba su sa kasashen yamma sun dauki batun da wani muhimmanci ba. Kawo yanzu ba wani dan siyasa a Turai da ya alakanta kanshi da wani bangare a yakin na Yemen inda manyan daulolin yankin Gabas Ta Tsakiya wato Saudiyya da Iran ke fito na fito, domin akwai babbar barazanar bata ran daya ko ma kasashen biyu da ke jagoranta yakin. Kamar yadda bangarorin biyu suka yi ruwa da tsaki a yakin Siriya, yakin kuma da janyo mastalar kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai.
Siriya dai ta fi kusa da Turai, Yemen kuwa na da nisa. Saboda haka dubun dubatan 'yan gudun hijirar Siriya sun shigo Turai, amma daga Yemen da yaki ya daidaita, ba dan gudun hijira ko guda da ya shigo Turai. Hakazalika ba bu wani dauki na a zo a gani da kasar ta Yemen da ke zama matalauciya a jerin kasashen Larabawa.
Yerima mai jiran gado a Saudiyya wato Mohammedm bin Salman na ci-gaba da jagorantar yakin babu kakkautawa, abin da ya kara jefa kasar cikin halin kakanikayi. Ita ma Iran a ranar Talata ta gargadi Saudiyya dangane da kai hare-haren Yemen tana mai cewa za ta nadama.
Su ma sauran kasashen yankin da ma wadanda ke nesa kamar su Pakistan da Indiya da ke can Gabas mai nisa da Yemen da su Habasha da Sudan da ke yamma da Yemen ba wani abin da suka yi da nufin kawo karshen rikicin.