1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Sabuwar dama a yankin Gabas ta Tsakiya

November 30, 2012

Ɗaga matsayin Falasdinawa a Majalisar Ɗinkin Duniya kyakkyawan mataki ne bisa turbar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. inji Kersten Knipp a cikin wannan sharhi.

https://p.dw.com/p/16ttS
Hoto: AFP/Getty Images

Sakamakon a bayyane ya ke. Ƙasashe 138 daga cikin jimillar membobi 193 suka goyi bayan buƙatar ɗaga matsayin Falasɗinu. Shin hakan na nufin wata nasara ce ga Falasɗinawa waɗanda suka kunyatar da abokiyar adawarsu a idon duniya? Ko kuma wani kaye ne ga Isra'ila wadda ta ƙuduri aniyar ganin bayansa ko ta halin ƙaƙa? Haka dai dukkan sassan biyu wato Isra'ila da Falasɗinu suka kwatanta sakamakon ƙuri'ar.

Tambaya a nan ita ce ko irin waɗannan kalaman za su taimaka? Ana iya kwatanta matakin a fuskoki dabam dabam, wato a matsayin babbar damar daidaita al'amura da samar da zaman lafiya a yankin. Musamman a matsayin wani ƙalubale ga Isra'ila.

Da yawa daga cikin 'yan Isra'ila na nuna shakka ko da gaske Falasɗinu take na neman zaman lafiya, matsayin da masharhanta ke ƙara bayyanawa. Yunƙurin Falasɗinu na samun amincewa ba komai ba ne illa neman kawar da Isra'ila, inji Shlomo Slonim masanin tarihi ɗan Isra'ila. Burin Abbas a fili yake, wato gusar da Isra'ila amma ba ya kafa wata ƙasar Falasɗinu da za ta yi zaman lafiya da Isra'ila ba. Saboda haka a gare shi bin hanyoyin diplomasiya tamkar wani yaƙi a kaikaice, inji Slonim.

Israel Demonstration Anerkennung Palästinas durch Vereinte Nationen
Isra'ilawa ba su daɗin matakin baHoto: Reuters

Falasɗinawa sun ɗauki ƙarin nauyi

Zai wuya a fahimci irin wannan adawar. Da wannan sabon matsayin, shugabannin Falasɗinu sun ɗauki wani sabon nauyi. Domin yanzu za su fi mutunta tsare tsare na ƙasa da ƙasa sannan zai zame musu dole su yi aiki da dokokin diplomasiya.

A dangane da manufofinta na gina matsugunan Yahudawa kuwa, bai kamata Isra'ila ta nuna wata damuwa ba. Idan Falasdinu, godiya ta tabbata ga sabon matsayinta, ta kai batun gaban kotun shari'a ta ƙasa da ƙasa dake birnin The Hague, hakan zai ba wa Isra'ila damar kare manufofinta a gaban kotu. Idan ya bayyana a fili cewa matsugunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa, ba abin da zai hana a saurari shari'ar a birnin The Hague. Dole ne a yi wa kowa adalci.

Shawara mai wuya ga Jamus

Matakin da tarayyar Jamus ta ɗauka na yin rowar ƙuri'a bai zo mata da sauƙi ba, kasancewa ba ta son marawa matsayin Isra'ila na adawa da buƙatar Falasɗinu. Ministan harkokin waje Guido Westerwelle ya ce ko da yake gwamnatin Jamus ta yi shakka cewa matakin Falasɗinu zai taimaka wa shirin zaman lafiya a yanzu, amma ya ƙara da cewa hakan ya dace da matsayin a kan rikicin, wato kafa ƙasashe biyu maƙota.

Deutsche Welle Nahost Kersten Knipp Kommentar
Sabuwar dama ga Gabas ta Tsakiya inji Kersten KnippHoto: DW

Gwamnati a Berlin ta san yadda za a karɓi matsayinta a Ramallah da ma ilahirin duniyar Larabawa. Kimanin mako guda da ya gabata Isra'ila da Falasɗinawa sun kawo ƙarshen wani rikici da ya halaka mutane fiye da 100. Yanzu a Majalisar Ɗinkin Duniya dake zaman cibiyar diplomasiya, kusan ƙasashe 200 suka kaɗa ƙuri'a a kan matsayin yankunan Falasɗinawa abin da kuma zai iya sake fasalin rikicin nan gaba.

Mawallafa: Kersten Knipp / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi