1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da mamayen Rasha a Ukraine

February 24, 2023

Shekara guda kenan da kaddamar da yaki a tsakiyar nahiyar Turai. Ta hanyar aikin 'yan jaridu ne kadai duniya ke sanin irin ukubar da jama'ar Ukraine suke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4Nwr1
Wladimir Putin da Wolodymyr Selenskyj
Wladimir Putin da Wolodymyr SelenskyjHoto: A. Gorshkov/SPUTNIK/AFP/Getty Images/Presidency of Ukraine/AA/picture alliance

Miliyoyin 'yan Ukraine sun fuskanci azabar yaki tun bayan da Rasha ta kaddamar da gagarumar mamaya a kan kasar shekara daya da ta wuce. 'Yan Jarida suna da hakki na baiyana gaskiyar mace-mace da ta'asa da kuma karfin imanin da ba zai gushe ba.

A birnin Bakhmut jini ne ya mamaye dusar kankara. Tsawon watanni sojojin Rasha suke ta fafutukar kwace dan karamin birnin da ke gabashin Ukraine. Sun yi ta kai hari ta bangarori da dama tare da tallafin sojan haya na Wagner marasa imani da tausayi. Gidaje da hanyoyi an yi musu luguden bama bama ba tare da la'akari da fararen hula da za su jikkata ba.

Kafin Rasha ta kaddamar da yakin na fin karfi da tsoka a Ukraine, mutane kusa 70,000 ne suka zaune a Bkhmut. Nawa ne suka rage a yanzu? babu wanda yake tabbaci. Sai dai wadanda suka rage sun ki mika wuya. Sojojin Ukraine sun ci gaba da yaki don kwatar yancinsu. Ba sa son barin Bakhmut a hannun makiya abokan gaba. Karamin garin na zama alama ta juriya da jajircewa na Ukraine.

Zahirin rayuwa a biranen Ukraine.

Manuela Kasper-Claridge
Manuela Kasper-ClaridgeHoto: DW/R. Oberhammer

Abin da ke faruwa a Bakhmut ya shafi dukkanin mu. Ba zai yiwu mu rufe idanunmu ga abin da ke faruwa a kasar Turai ba. Ana kisa, azabtarwa da fyade. Wannan yakin ba gaibu ba ne. A yaki ana mace mace da kuma jama'a fararen hula da lamarin ke ritsawa da su. Wannan ya faru a Bakhmud da Bucha da Irpin da kuma Mariupol.

A matsayin 'yan jarida muna da hakki na tattara bayanan wadannan ta'asa. Sai dai kuma duk da haka ya kamata mu yi taka tsantsan wajen zabar abin da za mu nuna duk da cewa bai kamata mu yi wa masu sauraro shamaki daga gaskiyar ta'asar da ke faruwa ba. To amma ya kamata mu kare martabar mutanen da aka aikatawa ta'asar.

Babu shakka muna, ba da rahoto  akan yadda al'umma fararen hula suke rayuwa a karkashin yanayi na barin a fagen da-ga. Yadda suke rayuwa yadda al'amura suka birkice kuma a haka suke samun lokacin nishadi da karfin hali.

Dole a kalubalanci farfagandar Rasha

Serhiy Bohdanovskyi
Serhiy BohdanovskyiHoto: privat

Mene ne gaskiya kuma mene ne karya? Ba abu  ne mai saukin baiyanawa ba. Musamman a wajen yaki. 'Yan jaridun mu suna da ke aiki a Ukraine suna aiki mai matukar wahalar gaske. Sai sun tantance hotuna da bidiyo tare da sauran abokan aiki, da yin magana da shaidun gani da ido da tantance gaskiya da bayar da bayanai da fallasa labarin karya. A lokaci guda kuma suna la'akari da hadarin su kansu lamarin ya ritsa da su.

Tasirin aikinsu ya fi gaban a baiyana. Shi ya sa masu mulkin kama karya suke jin tsoron irin wannan aiki na jarida mai zaman kansa.

Wannan ne ma ya sa 'yan farfagandan Putin suke kokarin amfani da duk wata kafa ta yada labaran karya domin boye gaskiyar lamari game da yakin fin karfi da Rasha  ke yi don ganin ba a wallafa shi ba yadda walau duniya ko kuma 'yan kasarsa ba su fahimci abin da ke faruwa a Ukraine ba. Haka ma da sanin hakikanin yawan mutanen da yakin ya tagaiyara ko kuma yawan hasarar  sojoji da Rasha ta yi.

Haka kuma yakin karon batta ce ta fito da gaskiya.

'Yan Ukraine da yaki ya ritsa da su
'Yan Ukraine da yaki ya ritsa da suHoto: NDR

Kalubale ne mai wahala shawo kan bayanan tunzuri da Rasha ke yadawa da gangan domin birkita hankalin jama'a. Akwai bukatar baiyana gaskiya. Yan jaridun DW da sauran abokan aiki daga sauran kafofin yada labarai suna sadaukar da rayuwarsu wajen baiyana wannan da kuma tabbatar da ganin gaskiya ta yi halinta.

Ga mutane da dama, shekara guda da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, gwagwarmaya ce ta kare kai domin 'yantar da kasarsu. Gwagwarmayar da ke bukatar tallafi da goyon baya daga dukkan wani dan nahiyar Turai).