Koriya ta Arewa da takwararta ta Kudu sun bai wa marada kunya inda bayan watanni na cacar baka suka tattauna kai tsaye tsakaninsu don magance rikicin da suke fama da shi. Babban matakin da suka dauka shi ne: Koriya ta Arewa za ta tura da 'yan wasa a gasar Olympik na lokacin sanyi da zai gudana a Koriya ta Kudu. Mai yiwuwa ma 'yan wasan kasashen biyu su jera hannu da hannu a bikin budewa da rufe gasar. Hasali ma dai, kamar a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da Koriya ta Kudu ta dauki bakwanci a 2002, harkokin wasanni sun sake zama wani bakin zare na warware rikicin makwabtan biyu.
Ba wai wasanni da Koriya ta Arewa da kuma Koriya ta Kudu za su halarta ba ne ke da muhimmanci, amma katse gabar da ke tsakaninsu bayan shekaru biyu na kai ruwa rana. Tuni suka amince da farfado da layi na musamman don tattaunawa ta wayar tarho kan harkokin da suka shafi tsaro. Kuma mai yiwuwa a yayin gasar ta lokacin sanyi, akwai haduwa ta iyalan da suka rabu tun karshen yakin 1953. Tuni Rasha da China da suke dasawa da Koriya ta Arewa suka yi na'am da wannan mataki.
Burin Kim ya cika
Wannan cigaban na da ban mamaki kasancewa shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un da shugaban kasar Amirka Donald Trump sun ta kalamai na batanci tsakaninsu a game da gwaje-gwajen makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi, lamarin da ya sa aka kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki. Sai dai a daya bangaren matakin bai zo da mamaki ba domin kuwa sai da Kim Jong-Un ya mallaki makamin nukiliya kafin ya koma kan teburin tattaunawa, lamarin da ya sa za a iya dangantashi da mai tsananin wayo.
Dole ne a bai wa Kim Jung-Un matsayinsa na wanda ya mallaki makamin da zai iya kai wa Amirka hari. Saboda haka ne kada Japan ta kuskura ta tsokani Koriya ta Arewa saboda ba zai jawo alhairi ba. Sai dai kuma babu wani dalilin da zai sa shugaban na Koriya ya yi amfani da makamin na kare dangi saboda Trump da yake dangantawa da "tsohon mahaukacin Amirka" ya yi barazanar share Koriya ta Arewa daga doron kasa.
Dama ga Amirka
Sai dai a Koriya ta Kudu, shugaban kasa Moon ya nuna murna kan tattaunawa tsakanin kasarsa da Koriya ta Arewa saboda hadewar kasashen biyu shigen na Jamus na daga cikin manufofin da ya sa a gaba. Amma da yake sassan biyu sun share fagen, abin da ya rage shi ne kasashen Amirka da China su kawo dauki domin a shiga babi na gaba na tattaunawa kan batun da ya shafi makamashi a lokacin da Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu za su sake zama kan teburin tattaunawa.
Ta wannan hanyar goyon bayan sulhu ne Amirka za ta iya sake dawo da martabarta ta uwa ma ba da mama a duniya tare da samun amincewar kasashen Asiya. Da ma dai an san cewar jerin takunkuman karya tattalin arziki da aka kakaba wa Koriya ta Arewa ba su yi tasiri ba. Saboda haka ne ake bukatar karawa da wasannin Olympik har lokacin da zaman sulhu zai yiwu. Sai dai idan aka yi la'akari da kai ruwa rana da aka yi ta yi da Koriya ta Arewa, an san cewa ko shakka babu shiga wasannin Olympik ya kasance babban nasara.