1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Zanga-zangar Iran

Mostafa Malekan
January 3, 2018

Tun shekaru biyu da suka gabata masana ke yin gargadin barkewar zanga-zanga a Iran inda suke cewa matsin tattalin arziki da na siyasa da kuncin rayuwa ka iya sa jama'a su bijire wa gwamnati inji Mostafa Malekan.

https://p.dw.com/p/2qGcy
Iran Protest in Teheran
Hoto: Fars

A yanzu wannan gargadi da hasashen da aka yi ya zama gaskiya, inda matsin ya sa jama'a suka hau kan titi suna bayyana fushinsu a cewar Mostafa Malekan na sashin Farsi a DW ya rubuta. Wannan shi ne abin da ya biyo bayan juyin-juya halin da aka yi shekaru masu yawa, inda kasar mai yawan al'umma kimanin miliyan 80, daga cikinsu a yanzu kashi 40 cikin dari ke rayuwa cikin talauci. Idan aka  shiga karkara, yawan talauci ya kai kashi 60 izuwa 70 a tsakanin al'umma. Matasa 'yan shekaru 15 izuwa 24 duk suna zaman kashe wando ba tare da aikin yi ba wannan kuma har da wadanda suka kammala karatu.

Barnar dukiya:

Iran ba kasa ba ce matalauciya ba, don kuwa a zamanin mulkin Mahmoud Ahmadinedschad na tsawon shekaru takwas, ya samarwa kasar dalar Amirka biliyan 700 daga sayar da danyen man fetur. Sai dai kaito ba dukkan kudin aka yi amfani da su wajen yaki da talauci a kasar ba. Kaso mai yawa na kudin an yi amfani da su wajen harkokin addini da kafa cibiyoyin yada akida, wanda gwamnatin kasar ke karewa. Wani kaso kuma an bayar da shi wajen inganta makamashin nukiliya da kuma samarwa sojojin kasar rokokin yaki. Yayin da wani bangaren kudi kuma aka yi amfani da su wajen kare gwamnatin Siriya da karfafa kungiyar Hezboullah a kasar Lebanon dama sauran kungiyoyin Shi'a a kasar Iraki da Yemen. A yanzu haka akwai ayyukan raya kasa da yawa wadanda suka tsaya cik, wanda da an yi amfani da kudin da ake samu daga kasashen ketare wajen farfado da wadannan ayyuka to da an samar ma dimbin matasa ayyukan yi.

Iran Demonstration für die Regierung
Hoto: Reuters/Tasnim News Agency

Rouhani ya ciza yatsa.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na 2013, lokacin da takaddamar nukiliya ta yi kamari,Hassan Rouhani ya yi yakin neman zaben da sunan magance rikicin Iran da kasashen duniya. To kodayake ya yi nasarar warware batun nukiliya da kasashen yamma amma kuma lamarin bai sauyaba, kamata ya yi ya tsaya yanzu wajen magance matsalar rayuwar jama'a. Abin da ya hana Rouhani nasara ta bangaren tattalin arziki kuwa, dalilai ne masu yawa. Na daya dai mahukuntan kasar sun yi matukar zuba kudi wajen inganta nukuliya, musamman gudun abin da ka iya faruwa bayan da Donald Trump ya lashe zabe a Amirka. Iran ta ji tsoron makomar huldarta da Turai, ga kuma karuwar zaman dar-dar a tsakaninsu da Saudiya, wadannan duk suna cikin abin da ya hana shugaba Rouhani cika alkawuran tattalin arziki da ya dauka.

Iran Demonstration für die Regierung
Hoto: Reuters/Tasnim News Agency

Karuwar fusata:

Zanga-zangar ta yanzu ta faro ne da batun tattalin arziki, sai dai cikin sauri ta koma na siyasa don neman sauyin gwamnati. Masu zanga-zangar ba su amince da tsarin da yanzu ke mulkin kasarsu ba. Wannan yanan cikin abin da ya sa zanga-zangar ta bazu cikin karamin lokaci. Matsalar talauci, rashin aikin yi da kyamar gwamnnati da tsare-tsarenta wadannan sune musabbabin zanga-zangar da ake yi. Zanga-zangar tana gudanan ne a birane da suka fi talauci. Amma kawo yanzu harkokin al'adu da na bangaren siyasar kasar duk ba abinda ya shafi zanga-zangar. Don haka wannan boren gwamnati za ta iya murkushe da karfi, sai dai in sauran al'ummar kasar suka shiga suma aka fara yi da su. Idan  lamarin ya yi kamari, makomar ita ce sojoji da sauran masu kishin kasar Iran za  su iya karbe iko da sauran al'amura, wanda kuma in hakan ta faru ba wai za'a magance matsalar talaucin da 'yan kasar ke fuskanta ba, sai dai kawai a kara karfi ga jami'an juyinjuya halin Iran, hakan zai kara jefa 'yan kasar cikin matsaloli fiye da wanda ake ciki a yanzu.

 

Wanda ya rubuta sharhin ya nemi kar sa hotonsa  bisa dalilan tsaro: