1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal
May 21, 2021

Taro tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron da wasu shugabannin Afirka a birnin Paris ya dauki hankalin kusan dukkan jaridun Jamus a sharhuna da kuma labaran da suka buga kan nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/3tnal
Frankreich Paris | Afrika-gipfel Emmanuel Macron und Bah N Daw
Macron da shugaba Bah N Daw na MaliHoto: Xose Bouzas/Hans Lucas/picture alliance

.A labarin da ta buga game da taron jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa sabuwar alkiblar Macron ga Afirka. Ta ce taron ya duba sabbin dubarun tallafawa Afirka domin hana sabuwar kwararowar 'yan gudun hijira saboda dalilai na tattalin arziki sakamakon annobar Corona. Ta ce ko shakka babu jerin mahalarta taron na birnin Paris na zama shaidar nasarar manufar da Shugaba Macron ya saka a gaba, cewa Faransa za ta daina mayar da hankali kan kasashen Afirka masu magana da harshen faransanci kadai domin kaucewa daga zargin da ake mata na bin sabon salon mukin mallaka. Saboda haka taron na duba irin tallafin da za a ba wa Afirka don rage radadin tawayar tattalin arziki sakamakon annobar Corona, inda aka gaiyaci shugabannin kasashen Afirka 15 da suka hada da na Afirka ta Kudu da Angola da Mozambik da Ruwanda da kuma Najeriya.

Frankreich Emmanuel Macron und Abdalla Hamdok
Macron da Firaministan Sudan Abdalla HamdokHoto: Ludovic Marin/AFP

A sharhin da ta yi kan taron kolin jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi baya ga tallafin kudi don ta da komadar tattalin arzikin Afirka, taron na birnin Paris ya kuma duba batun yafe basussukan da ake bin kasashen Afirka. Jaridar ta ce a wani abin da ke zama somin tabi, a jajiberen taron, Faransa ta yafe wa kasar Sudan bashin Euro miiyan 5000, Jamus ta bi sahu da yafe Euro miliyan 360. Za kuma ta biya mata bashin Euro miliyan 90 da Asusun IMF ke bin Sudan din. Sai dai ba duka mahalarta taron ne ke da ra'ayin cewa yafe bashin shi ne mataki mafi a'ala ba.

Ministan kudin Jamhuriyar Benin Romual Wadagni ya nuna shakku yadda ake duba cancantar kasar kafin a ba ta bashi. Yana mai cewa daga baya ana cinsu tara, wanda hakan ke tauye kokarin da kasashe ke yi na inganta yanayin kasuwanci da cika ka'idojin masu ba da rance

Frankreich Gipfel Abdel Fattah el-Sissi und Emmanuel Macron
Abdel Fattah el-Sissi da shugaba MacronHoto: Christophe Ena/AP Photo/picture alliance

Kungiyar Tarayyar Turai, EU, za ta taimaka a gina kamfanonin harhada magungunan riga-kafi a Afirka, don hana kasashe matalauta dogaro da sayen alluran riga-kafi daga ketare, inji jaridar Süddeutsche Zeitung.

Jaridar ta ruwaito shugabar hukumar kungiyar EU, Ursula von der Leyen a taron kolin Faransa da Afirka a birnin Paris, na alkawarta kaddamar da wani shiri da zai ba wa kasashen Afirka damar samar da magungunan riga-kafi da kansu domin ta inganta tare kuma da fadada fannonin kiwon lafiya da dukkan bangarorin da ke da nasaba da wannan fanni.

Ko da yake mafi rinjaye na kasashen EU na adawa da matakin, amma jaridar ta ce wannan shiri ga Afirka na sake nuna cewa samar da magungunan riga-kafi ga kasashe matalauta yana da matukar muhimmanci ga EU. Za dai a dauki lokaci mai tsawo kafin a gina masana'antu da EU za ta ba da kudi da kwararru da kuma fasahohin yin su.