Sharhin Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka
April 12, 2024A sharhinta mai taken:"Brussel ta biya kasashen Mauritaniya da Tunisiya da Masar kudidomin takawa 'yan gudun hijira birki," jaridar die Tageszeitung ta ce yarjejeniyar EU da Tunisiya da sauran kasashe na cike da cece-kuce, bayan shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta sanya hannu a kan dokar a birnin Brussel.
Majalisar Tarayyar Turai ta yi kira ga Hukumar nahiyar da ta yi bayani dalla-dalla kan kudin da aka biya da kuma yadda kasashen ya kamata su bayar da gudummawarsu, domin cimma manufofin da aka sama gaba na hana kwararar bakin haure.
Mace ta zama firaminita ta farko a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
A karon farko an nada mace ta farko a matsayin firaminista Judith Suminwa Tuluka a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Wannan shi ne taken da jaridar Frankfurter Allgemeine ta wallafa a sharhin da ta ce Suminwa mai shekaru 56 har yanzu tana mamaki da wannan nadi wanda sotari yan jamiyyar UDPS jam'iyyar shugaban kasar ake bai wa wannan matsayi.
Sun dai hadu da shugaba Félix Tshisekedi a Brussels, inda suka yi karatu a farkon shekarun 1990. ta yi aiki a hukukmar UNDP ta Majalisar Dinkin Duniya kafin ta rike matsayin ministar tsare-tsare.
Jarida ta Frankfurter Allgemeine ta ce sabuwar firaministan sai ta samu kwarin gwiwa daga shugaban kasar domin tinkarar al‘amarin da ake fama da shi a yankin gabashin kasar na yaki da kungiyar ‘yan tawaye ta M23. Jaridar ta ce bayan nadin da aka yi mata yayan jam'iyyar ta UPDS sun yi ta yi gunaguni amma ta ce Shugaba Felixe ya yarda da aikin wannan mata shi ya sa ma ake ganin za ta samu nasara duk da ma yadda akwai wadanda ba su so nadinta ba.
Akwai alamun Faransa za ta rasa karfin fada aji a kasar Senegal
Faransa ba ta son rasa Senegal. Amma kuma sabon shugaban kasar Bassirou Diomaye Faye yana da raayin yaki da yan mulkin mallaka wannnan shi ne taken da jaridar Welt Online ta buga a sharhin da ta yi kan Senegal.
.A cikin wani gajeran saƙon, masu sukar Faransa kamar su Nathalie Yamba wata yar fafufutuka yaki da mulkin mallaka yar kasar Kamaru da kuma Kemi Seba dan kasar Benin sun yin murna da zuwa Diomaye a kan mulki. Su dukkanisu suna da alaƙa da yawa da Rasha sun kuma ce zaɓen Faye wata alama ce mai ƙarfi ga duk azzalumai, 'yan mulkin mallaka waɗanda a halin yanzu ke kan gaba a ƙasashenm Afirka.
Tarihin kisan kiyashi a Rwanda ba zai taba shafewa ba
Ruwanda tarihin da ba zai taba bacewa ba.wannan shi ne sharhin da jarida die Welt ta bude sharhinta da shi a cikkar shekaru 30 da yin kisan kare dangi na ‘yan kabilar Tutsi daga ‘yan hutu. An yi kisan kare dangi a Rwanda daga ranar 6 ga Afrilu zuwa 4 ga Yuli, 1994. A cikin kwanaki 100 kacal, an kashe kusan mutane dubu 800,000, musamman daga kabilar Tutsi. Jaridar ta ce shekaru 30 bayan wannan yaki har yanzu akwai balshensa na marayu da wadanda suka samu tabin hankali
Shin wadan ne irin muhimman darussa za a iya amfani da su don magance wannan matsala, da kuma hana tashin hankali a nan gaba ta ce wannan shi ne irin abin da har yanzu ake kokarin cimma a kowace shekara a bikin jimamin na tunawa da wannan kisan kare dangi akan yi tunani kara samar da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya na barkewar yakin.