Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka
March 3, 2023Taken jaridar Die Tageszeitung da ta rubuta shi ne, ''Tinubu ya zama sabon shugaban Najeriya'' Tsakar dare Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ayyana Bola Ahmed Tinubu, dan takarar jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben. Sai dai jam'iyyun adawa na son kalubalantar sakamakon. Ta ce, za a iya cewa a birnin Lagos al'amura sun dan saisaita zuwa wani lokaci da safiyar Larabar wannan mako. Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana Tinubu mai shekaru 70 da haihuwa a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata.
Dan takarar jam'iyya mai mulki ta APC ya lashe zaben da kuri'u miliyan takwas da dubu 800, wato kimanin kaso 36 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Da misalin karfe biyar da rabi na safe, Tinubu ya yi jawabin godiya yana mai cewa: "Ina gode muku baki daya, tilas mu yi aiki tare domin tabbatar da lafiyayyiyar Najeriya." A karon farko a tarihin siyasar Najeriya, 'yan takara uku sun fafata a tsakaninsu da kuma yawan kuri'un da suka samu ya kasance mai yawa. Jaridar ta ce, a birnin Lagos an samu karancin cunkoso, saboda kowa na taka-tsan-tsan na rashin sanin abin da kaje ya zo. Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ne ya zo na biyu da kaso 29 cikin 100, yayin da Peter Obi na jam'iyyar Labour ya zo na uku da kaso 25 cikin 100. Ita ma dai jam'iyyar NNPP da tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Dakta Rabiu Kwankwaso ya kafa, ta samu tagomashi a arewacin kasar duk da kasancewarta sabuwa.
Shugaban kasa mai tarin dukiya, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Ta ce, sabon shugaban Najeriya mutum ne da bai cika magana ba, koda masu nuna adawa da shi ba su da abin fadi mai yawa a kansa. Mai shekaru 70, a lokacin da aka tambaye shi dalilin da yake ganin ya sanya al'umma zabarsa sai ya ce: "Ni na dabam ne, ni ne Bola Ahmed Tinubu." A ganinsa alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa, sun kasance kadan masu amfani. Sune, bunkasa tattalin arziki da ayyukan yi da rage tsadar kayayyaki. Haka kuma dan takarar da ke da muhimmanci, bai halarci duk wata muhawara da aka shirya a gidan talabijin gabanin zabe ba.
A wuraren da ya bayyana a bainar jama'a kuwa, ya yi kalaman da ba lallai ne masu sauraronsa su fahimce su ba. Wa'adi biyu da ya yi a matsayin gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 da 2007, sun sa an saka masa sunan "Dan Birnin" ko kuma "City Boy" Tinubu na cikin mutane masu arziki a kasarsa, domin kuwa yana ma da gidajen da yake bayarwa haya. Ya fara siyasa a matsayin dan adawa tun lokacin mulkin danniya na sojoji. Tsohon shugaban mulkin soja na kasar marigayi Janar Sani Abacha ya tilasta masa yin hijira, kuma sai bayan da Abacha ya rasu a shekara ta 1998 sannan ya koma gida Najeriya.
Jaridar Süddeutsche zeitung da ta rubuta sharhinta mai taken: Faransa; "Afirka ba bayan gida ba ce." ta ce: Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na ziyara a Afirka. Kafin nan ya bayyana aniyar kasarsa ta rage yawan sojojinta a Afirka, sake sabon tsari? Jaridar ta ce ba wannan ne karon farko da Macron ke zuwa Afirka ba. Kimanin sau 14 ke nan, koma fiye da hakan. Tafiyar ta shugaban Faransan ta wannan karon na da matukar muhimmanci, inda zai ziyarci kasashe hudu da suka hadar da Gabon da Angola da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.