Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka
June 9, 2023Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta soma sharhinta da cewa, zanga-zanga da mace-mace a Senegal. Hukuncin da aka yi wa madugun 'yan adawa ya haifar da tarzoma. Bakin hayakin kona tayoyin mota, motocin 'yan sanda masu sulke su ne kawai ake gani a Dakar babban birnin kasar ta Senegal. Kafafen yada labarai a kwanakin nan sun watsa hotuna marasa kyaun gani a tarzomar ‘yan sanda da masu bore. Jaridar ta ce, wannan dai ba saban bane a kasar Senegal. Boren ya biyo bayan hukuncin da aka yanke wa madugun 'yan adawa Ousmane Sonko.
A sharhinta jaridar Die tageszeitung ta ce, Somaliya a kan kogin Nilu a Sudan, masu fada a ji na wargaza kasarsu, kamar yadda a Somaliya ke yi fiye da shekaru talatin da suka wuce. Kuskure daga wancan lokacin, bangaren kasa da kasa ne ke ta maimaitawa. Sanin tarihi na baya-bayan nan na Afirka ya na da ma'ana. 'Yan tawaye sun yi maci suna murna da sunan nasara har zuwa babban birnin da rikici ya raba gida biyu. Girman kai ya bayyana a fili cikin wannan dan gajeren lokaci na fara rikicin Sudan, wanda duk abin da ya kawo shi, shi ne rashin adalci. Yanzu Sudan ta shiga wani rikicin ba wanda kan iya kiyasin karshensa. Baki daya 'yan kasashen waje na ta tserewa, su kuwa talakawan kasa na ta neman mafaka a inda suke iya samu. An kulle manyan shaguna da ma’aikatu da ofisoshin jakadancin kasashen waje, an sauke tutoci an kona takardu, an hau jirgi. Sudan dai yanzu ta shiga rashin tabbas.
Jaridar Die Welt ta ce, dabarar Ruwanda ta zama zakaran gwajin dafi ga Tarayyar Turai a tsarinta na takaiata shigowar 'yan gudun hijira. Jaridar ta ci gaba da cewa, Birtaniya na son hana bakin haure zuwa kasarta, kuma don cimma wannan manufar kasar na yin duk iya karfinta. Don haka, ya kamata a gudanar da hanyoyin neman mafaka a Afirka. Za a sake fara jigilar 'yan gudun hijra daga Birtaniya izuwa Ruwanda nan ba da jimawa ba. Masana na kallon dabarun a matsayin "Abun gwaji" ga Tarayyar Turai.
Sai Die Welt ta ci gaba da batun takin zamani a Afirka. Jaridar ta ce, yakin Ukraine da Rasha mai taimaka wa nahiyar Afirka ta fannin noma. Jaridar ta ce a yayin da yakin da Ukraine ke tsawaita, Afirka na kara shiga matsalar karancin abinci. Rasha ta aike da takin zamani izuwa Afirka, inda jiragen ruwan kasar ta Rasha suka sauka tashar jiragen ruwan Nairobin kasar Kenya dauke da kayan gona. Sau da yawa ana zagin kasashen yamma ’yan siyasarsu, amma a wannan karo sun samu abun yin biki. In da aka hango ministan noma na kasar Kenya tare da jakadan kasar Rasha, sun siga cikin jirgin ruwan dakon kaya a Mombasa, in da suka bude kayan da ke kan jirgin wanda tarin takin zamani ne. Don haka yanzu Rasha na da abun fada, in da take nuna cewa, ba wai abinci kawai take iya bai wa Afirka ba, amma hatta kayan noma za su rika samu daga Mosko.