Shari´ar Charles Taylor
June 1, 2007Kotun ƙasa da ƙasa dake gudanar da shari´ar lefin kissan ta ce ta shirya tsap! Dominfara shari´ar tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, tun ranar litinin mai zuwa.
Kotun a na tuhumar Taylor, da manyan lefika ɗaya na bin ɗaya har guda 11, da su ka haɗa da kissan gilla, fyaɗe, ta´adanci , handama,zalunci da dai sauran su,a lokacin yaƙin basasar da ya wakana a Sierra Leone daga shekara ta 1991 zuwa 2002.
Shugaban kotun ƙasa da ƙasar dake birnin Hage, wato Stephen Rapp, ya ce za a kammala wannan shari´a a cikin wattani 18.
Idan dai ba a manta ba, a shekara ta 2003 ne Charles Taylor,ya sauka daga karagar mulkin Liberia, ya kuma samu mafaka a Taraya Nigeria, saidai a shekara da ta gabata, bisa matsin lambar manyan ƙasashen dunia, shugaba Olesegun Obasanjo, ya tasa ƙeyar sa zuwa kotu.
Kasar Britania ta yi tayin karbar Charles taylor a gidan kurkuru da zaran kotu ta kammala shari´ar.