1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shari'ar kan tsige mataimakin shugaban Kenya

Suleiman Babayo MAB
October 22, 2024

A kasar Kenya wata babbar kotu ta fara sauraron karar da Rigathi Gachagua mataimakin shugaban kasar da aka tsige ya shigar, inda ya kalubalanci matakin majalisar dokoki na raba shi da mukamun.

https://p.dw.com/p/4m68X
Kenya | Nairobi | Rigathi Gachagua
Rigathi Gachagua mataimakin shugaban kasar Kenya da aka tsigeHoto: Andrew Kasuku/AP Photo/picture alliance

A wannan Talata babbar kotun kasar Kenya ta fara sauraron karar mataimakin shugaban kasar da aka tsige Rigathi Gachagua  ya shigar inda yake kalubalantar matakin na tsige sakamakon kuri'ar da majalisar dattawa ta kada a makon jiya.

Shi kansa Gachagua mai shekaru 59 da haihuwa ya halarci zaman kotun kuma ya musanta zargin da aka masa, da suka hada da neman kawo rikicin kabilanci saboda kalamansa da yake yi gami da wasu batutuwa da suka saba dokokin kasar.

Jim kadan bayan tsige Rigathi Gachagua daga mukamun na mataimakin shugaban kasar Kenya, sai Shugaba William Ruto ya gabatar da sunan ministan cikin gida, Kithure Kindiki, domin zama sabon shugaban kasa kuma majalisar dokoki ta amince da shi, amma aka gaza rantsar da shi saboda umurnin kotu na sauraron mutumin da aka tsige daga mukamun na mataimakin shugaban kasar ta Kenya.