1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar rikicin jam'iyyar MNSD Nasara a Nijar

Mamman KantaApril 16, 2015

A jamhuriyar Nijar a ranar Larabannan ne wata kotu a birnin Yamai,ta yanke hukuncin shari'ar rikicin jam'iyyar MNSD Nasara ta madugun adawa Alhaji Seini Umaru.

https://p.dw.com/p/1F8zv
Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Alhaji Seini Umaru na jam'iyyar MNSD Nasara madugun adawaHoto: DW/M. Kanta

Hukuncin kotun ya halatta wa Alhaji Seini Umaru jam'iyar, ya kuma haramta wa Albade Abuba jam'iyyar.

Dubban magoya bayan jam'iyyar ne suka yi cincirindo a harabar kotu don sauraron sakamakon shari'ar da aka yi ranar 11 ga watan Maris din da ya gabata, a kan rikicin da ake tsakanin tsohon babban sakatare janar din jam'iyar Albade Abouba, da shugaban jam'iyyar Alhaji Seini Oumarou, wanda kotun ta ba shugaban jam'iyyar gaskiya akan wannan shari'ar. Honnorable Tijjani Abdulkadiri,sabon babban sakatare janar din jam'iyyar cikin tashin tsika ya bayyana nasara cikin hukuncin da kotun ta yanke.

Alkalai sun ce wannan taron da abokan hamaiyar su suka yi haramtacce ne. Na biyu karar da taron da uwar jam'iyyar ta yi musu halar ne. Kuma tilas ne su yi aiki da wannan kudurin hukunci. Saboda haka sun gamsu da wannan shari'ar.

A nasu waje magoya bayan da ke cike da murna, sun ce sun ji dadin wannan shari'ar saboda basu gaskiya. Kuma sun jinjina wa alkalai a dangane da yanke hukunci da suke, kuma sun kira ga alkalan da su ci gaba da tsage gaskiya shi zai kawo zaman lafiya.

Niger - Politiker Albade Abouba
Albade Abouba tsohon babban sakatare janar din jam'iyar MNSD NasaraHoto: DW/M. Kanta

Tuni a cibiya jam'iyar magoya bayan jam'iyar ke ci gaba da shaugulgulan murna.

A wajen bangaren abokan hamaiyyar kuwa wato Albade Abouba,don jin ta bangaren su, Honnorable Sani Mai Goshi, ya ce basu sami takardar hukuncin kotun ba, don sani hukuncin da kotun ta yanke. Amma da zarar sun same ta, zasu kira manema labarai don bayyana aniyar su.

A yanzu ana jiran sakamakon shari'a biyu da aka yi daya kawar jam'iyar MNSD wato CDS Rahama. Shi ma jayaiyar ce tsakanin shugaban jam'iyar Mamane Ousmane, da Abdou Labo wanda Usman ya kai kara a kotun kungiyar gamaiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato CEDEAO, shari'ar da za'a yi ranar 23, da 25 ga watan afrilun nan.