1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shari'ar rusa kaburburan waliyyai a Mali

Gazali Abdou Tasawa
July 14, 2020

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa ta ICC za ta soma zaman shari'ar rusa kaburburan waliyyai a birnin Tumbuktu na kasar Mali da ke a karkashin kulawar hukumar ilimi da raya al'adu ta UNESCO.

https://p.dw.com/p/3fHGC
Zerstörung in Timbuktu
Hoto: picture-alliance/dpa/De Poulpiquet

A wannan Talata ce kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC ke soma zaman shari'ar mutumin nan mai da'awar jihadi da ake zargi da ba da gudunmawa wajen rusa hubbaren waliyyai a birnin Tumbuktu na yankin Arewa maso yammacin kasar Mali a shekara ta 2012 da 2013.

Kotun ta kuma zargin mutumin mai suna Al-Hassan Ag Abdoul Aziz Ag Mohamed Ag Mahmoud mai shekaru 42 da aikata laifukan yaki da cin zarafin dan Adam, da kuma laifin fyade da cin zarafin mata ta hanyar yi masu auren dole a lokacin da yankin na Tumbuktu ya fada hannu kungiyoyin 'yan ta'adda masu da'awar jihadi.

A watan Afrilun 2018 ne dai mahukuntan kasar ta Mali suka mika mutumin ga kotun ta ICC. Dama dai a shekara ta 2016 kotun ta ICC ta yanke hukuncin zaman sarka na shekaru tara ga Ahmad Al Faqi Al Mahdi wani mai da'awar jihadin na kasar Mali da ta samu da laifin rusa kaburburan waliyai a Tumbuktu.