1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor

Yahouza SadissouApril 4, 2006

Kotun ƙasa da ƙasa ta Siera-Leone ta gurfanar da Charles Taylor

https://p.dw.com/p/Bu0r
Hoto: AP

Haƙiƙa kotun Siera -Leone, kotu ce ta mussaman , kamar irin kotunan da ke gudanar da, shari´ar lefikan yaƙe- yaƙen ƙasashen Yugoslavia da Ruanda.

ƙasar Siera –Leone ta naɗa 4, daga cikin alƙalai 11, da kotun ta ƙunsa, sannan sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan ya naɗa sauran 7.

Yawan alkalan 11, ya zo daidai da yawan masu gabatar da ƙara su ma, su 11.

A game da wannan shari´a, ga abinda Jan Wetzel, wani sannanen alƙali na Bonn ke faɗa:

Babban darassin da mu ka ɗauka a nan Jamus, bayan shari´ar kotun ƙasa da ƙasa ta Nürberg ,wace ta yi shari´ar masu leffikan kunna rikicin yaƙe-yaƙe, bayan yaƙin dunia na 2, da kuma kotunan Ruanda, da na Yugoslavia, shine cewar irnin wannan shari´a na da sarƙƙaƙiya mattuƙa, kasancewar shari´ a ce, da ta shafi, wata ƙasa amma kotunan ƙasa da ƙasa, su ka ɗauki yaunin gunadar da ita.

Maimakon jama´a, ta zanƙi nuna ɗari ɗari, ga wannan kotuna, kamata tayi ta bada haɗin kai, ta kuma ɗauki cewar kotuna ne, da su ka shafe ta, bai wai na wata ƙasa ba,ko wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa daga ƙetare.

Amma a kasar Sirea Leone al´umma bisa alamu ta amince da wannankotu ta mussamman tare da ƙwadiyin ganin ta bayyana gasikiya, tare da hukunta mutanen da su ka kunna wutar rikicin.

Bayan kawo ƙarshen shi wannan yaki a yanku haka, yanzu haka jama´ana dauke da tabon sa.

Kazalika, har ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar, ba su aiki irin yadda ta kamata, inji Wetzel, a game da haka wannan kotu ta mussaman da aka girka, ta zama tamkar lantarki.

Da farko, mutane 13 ne, wannan kotu ke tuhuma da aikaita leffikan yaƙin Saleo, ya zuwa yanzu , 9 sun gurfana, an yanke wa 2 da ga cikin su, hukuncin kissa, mutun ɗaya ya tsere, sannan yanzu kotun ta fara sauraran Charles Taylor.

Ko wane irin hukunci ne, a ra´ayin mai shari´a, Jan Wetzel zai iya hawa kan Charles taylon ?

A nan, a iya sannin cewar Charles Taylor, a misali ya talafawa tsofuwar ƙungiyar tawayen RUF ta Siera Leone, da makamai da horo, kazalika ya taimaka, ƙwarai wajen tsara passalin yaƙe yaƙe, da kashe kashen jama´a.

Wannan babar matsala ce.