Shari'ar tsoffin magabatan yankin Kataloniya
November 2, 2017Talla
Kiran na zuwa ne, bayan gurfanar da sunayen jami'an bisa zarginsu da tawaye da tayar da rikici da satar dunkiyar gwamnati.
Wannan shari'a ta taso ne, biyo bayan ayyana 'yancin kai da majalisar dokokin Kataloniyan ta yi ne a ranar 27 ga watan Oktoba. Rahotanni na nuni da cewar, masu shigar da karan, sun nemi daure takwas daga cikin jami'an ba tare da bata lokaci ba, kana saura jami'i dayan, na iya zaman beli idan ya biya tsabar kudi euro dubu 50.
Tsohon mataimakin shugaban Kataloniya Oriol Junqueras, na cikin mutane takwas da kotun Spain ke nema.
A yanzu haka dai tsohon shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemon da ministocinsa hudu da ke zaune a kasar Beljium, sun watsi da umurnin bayyana a gaban kotun Spain din a yau Alhamis.