Shawarar samar da tudun mun tsira a Siriya
October 22, 2019Talla
Ministar tsaron kasar ta Jamus kana shugabar Jam'iyyar CDU mai mulki, ta bayyana hakan ne a wata fira da tashar DW inda amma ta ce shirin na bukatar samun goyon bayan Turkiyya da Rasha.
Ministar ta ce yankin da za a samar zai taimaka ga hana yaduwar ayyukan kungiyar 'yan ta'addar IS da kuma wanzar da zaman lafiya a yankin baki daya. Ministar ta kara da cewa majalisar dokokin kasar ta Jamus za ta yi nazari a game da yiwuwar aikawa da sojojin kasar a yankin.
Makonni biyu da suka gabta ne dai rundunar sojin Turkiyya ta kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawan yakin na Kungiyar YPG da nufin kwace yankin da ke hannunsu dan mayar da shi wani sabon matsugunnin miliyoyin 'yan Siriya da ke zaman gudun hijira a Turkiyya.