Nijar: Shawo kan matsalar dimukuradiyya
January 7, 2022Wannan tsari ya fito ne daga nazarin kungiyar Alternative Espaces Citoyens da masu hannu da shuni da ke kamawa, domin ganin ana shirya irin wannan tattataunawa a kowane farkon wata. Ana dai gayyoto masana daga jami'a da ma sauran bangarori, domin tafka muhawara da nufin samun haske ta yadda mafi yawan al'umma za su karu da zama. Taken wannan muhawara dai shi ne siyasa da rikice-rikice ko amfani da karfi, inda ake son a san wai shin mai ya sa har yanzu ita siyasa da aka kirkirota domin a zauna lafiya cikin tsari na doka, sai ake ganin akasin haka musamman a kasashen Afirka? A cewar Farfesa Mahaman Tidjani Alou na jami'ar Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar din, lamari ne mai sarkakiya: "Lalle sanin kowa ne batun rikici ko amfani da karfi ko daga bangaren gwamnati ko kuma wani bangare na al'umma, abu ne da ake yawan samu a cikin zamantakewa ta yau da kullum ta siyasa. Kuma abin da ya kamata a sani a cikin irin wannan yanayi, fahimci halin da ake ciki sannan a fahimci dalilan da suke sa wadanda abin ya shafa suke amfani da karfi cikin lamarin siyasa. Batu ne da ya kamata a san dalilinsa, kuma a irin wannan tattaunawa za a samu amsar tambayoyin."
An samu halartar matasa musamman wadanda ke karatu a makarantar horon matasa kan akidoji na dimukuradiyya da take hakkin dan Adam, inda a ta bakin Abdoulnasser Nahantsi Diori idan ka ga ana samun rikici a tafiyar siyasa to wani na yaki ya tsarin doka ko kuma ya yi son kai. Ana iya cewa shirya irin wannan muhawara da a cikinta aka gayyato masana irin su Farfesa Mahamane Tidjani Alou da Dakta Souley Adji masanin zamantakewar al'umma wanda dukkanninsu malamai ne a jami'ar birnin Yamai da kuma Farfesa Salim Mokaddem mai bai wa shugaban kasa Mohamed Bazoum shawara a fannin ilimi, babbar dama ce ta rabe zare da abawa a fannin samun hanyoyin magance matsalolin da ke hana ruwa gudu a fannin siyasa a kasashe kamar Jamhuriyar Nijar.