1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da abkuwar bila' in Fukushima

March 11, 2012

Al'umar Japan sun yi addu'o'i ga mutanen da su ka rasa rayuka cikin tsunamin Fukushima.

https://p.dw.com/p/14J3b
Japanese Emperor Akihito, left, and Empress Michiko attend the national memorial service for the victims of the March 11, 2011, earthquake and tsunami in Tokyo Sunday, March 11, 2012. Through silence and prayers, people across Japan on Sunday remembered the massive disaster that struck the nation one year ago, killing just over 19,000 people and unleashing the world's worst nuclear crisis in a quarter century. (AP Photo/Yoshikazu Tsuno, POOL)
Hoto: AP

Yaune ƙasar Japan take cika shekara guda, tun bayan bala'in tsunami, da ya faru a gaɓar tekun ƙasar, Jama'a za su yi tsit a dai-dai ƙarfe 2:46 na yamma a gogon ƙasar ta Japan,domin tunawa da mutanen da igiyar tsunami ta ritsa da su. Kazalika akasarin ababen hawa kamar su jiragen ƙasa duk za su tsaya cik a wannan lokacin. An dai yi ƙiyasin aƙalla mutane 19000 bala'in ya hallaka yayin da ya tilastawa wasu dubban mutane rasa gidajensu. Daga bisani ambaliyar ruwan ta haddasa tsayawar na'urorin rubbun makamashin nukiliya dake Fukushima, bayan da na'urorin sanyaya injin din suka daina aiki.

Mawallafi:Usman Shehu Usman
Edita: Yahouzua Sadissou Madobi