Shekara guda da fara yakin Rasha da Ukraine
A ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, al'ummar Ukraine suka wayi gari da tashin bama-bamai daga kasar Rasha.
Bakar rana ga miliyoyin al'ummar Ukraine
A ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, al'ummar Ukraine suka wayi gari da tashin bama-bamai. Sojojin Rasha sun mamaye kan iyakokinsu da Rashan da ma Belarus da kuma yankunan da Rashan ta mayar da su karkashin ikonta tun shekara ta 2014. An kai hari a Ukraine, tuni aka fara hadawa da hukumomin gwamnati da kuma ya fara shafar al'umma.
Hare-haren rashin imani
Shugaba Vladmir Putin na Rasha, ya bayyana harin da "matakin soja na musamman". Yana son karbe iko da yankunan Donezk da Luhansk. Mazauna birnin Mariupol, sun kwashe mako guda a ginin karkashin kasa na gidajensu. Da dama sun mutu a karkashin gine-ginen da suka rushe, kamar wasu daruruwa da suka mutu a karkashin baraguzan ginin wani gidan kallo.
Miliyoyi sun yi gudun hijira
Yakin na Ukraine ya janyo kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Turai, wanda ba a taba gani ba tun yakin duniya na biyu. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR ta ce, zuwa watan Fabarairun 2023 'yan gudun hijirar Ukraine a Turai sun fi miliyan takwas. Poland ta karbi sama da miliyan daya da dubu 500. Miliyoyi daga yankin gabashi da kudanci, sun watsu a sassan kasar.
Karbe iko da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia
A makon farko na mamayarta, Rasha ta karbe iko da yankuna da yawa a kudanci da gabashin Ukraine da ma wani bangare na arewaci musamman kusa da birnin Kyiv. Tun daga wannan lokaci, babbar tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia da ke yankin kudanci ke karkashin ikon Rasha. Yakin ya shafi farfajiyar tashar. Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA ta ce a sanya shingen kariya.
Ba a san adadin wadanda suka rasa ransu a yakin ba
Babu wanda ya san adadin wadanda suka rasa rayukansu a yakin. Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin fararen hula dubu bakwai da 200 da kuma sojoji dubu 12 sun halaka. Sai dai ta ce, adadin ka iya fin haka. Ba a san yawan sojojin Ukraine da suka halaka ba. A watan Disamabar bara, mai bai wa shugaban kasar shawara Mykhailo Podoljak ya ce sun kai dubu 13. Sai dai babu tabbaci kan adadin.
Tashin bama-bamai a gadar Crimea
A farkon watan Oktbar 2022, an samu tashin bama-bamai a gadar yankin Crimea da Rasha ta mamaye. Bama-baman sun lalata wani bangare na gadar da fadar Kremlin ta gina, a kan titin Kerch. Rashan dai ta ce, wata mota ce makare da bama-bamai daga Ukraine ta tashi a gadar. Sai dai tuni mahukuntan Kyiv suka mjusanta wannan zargi.
Munanan hare-hare a tashar samar da hasken wutar lantarki
Kwanaki kalilan bayan tashin bama-bamai a gadar Crimea, Rasha ta kai mummunan hari na farko a kan tashar samar da hasken wutar lantarki. Matsalar ta fi shafar biranen Lviv da Kharkiv. Tun daga lokacin, harin ya zama na yau da kullum. Saboda mummunar barnar da harin ya yi a tashar, kusan a baki daya Ukraine ana fama da rashin hasken wutar lantarki ko ruwa ko kuma abin dumama daki a kowacce rana.
Yaki da kuma sajewa cikin kasashen Turai
Volodymyr Zelenskyi na aika sakon faifen bidiyo a kullum tare da bayyana halin da kasar ke ciki, kuma miliyoyin mutane na kalla. Shugaban ba wai daga al'ummar kasarsa Ukraine kadai ba, ya ma samu taimakon daukacin kasashen yammacin duniya. A karkashin jagorancinsa, sajewa da kasashen Turai ya kai wani matsayi. A yanzu, Ukraine na neman zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai EU.
Ukraine na fatan samun motocin yaki kirar Leopard-2
Yadda Ukraine za ta iya karawa da Rasha, ya dogara ne ga taimakon da za ta samu. Kasashen kawance karkashin jagorancin Amurka, na samar da miliyoyin dalar Amurkan ga fannin tallafin jin-kai da kudi da kuma sojoji. An tafka gagarumar muhawara kan aika manyan makamai, a tsakanin kasashen Yamma saboda tsoron matakin da Rasha za ta dauka. Amma Ukraine na son samun manyan tankokin yaki kirar Leopard-2.