Shekara guda da kama mulkin Hollande a Faransa
May 17, 2013Talla
Shugaban Francois Hollande na Faransa ya bayar da shawarar ci gaba da hada karfi da karfe tsakanin kasashe da ke amfani da takardar kudin EU domin ceto nahiyar Turai daga matsalar kudi da ke addabarta a yanzu. Shugaban ya bayana haka ne lokacin wani taron manaima labarai da ke zama irin na biyu da ya gudanar a Paris tun bayan darewarsa kan kujerar mulkin Faransa. Holland ya ce kafa abin da ya kira wata gwamnatin mai cin gashin kanta da za ta kula da fannin tattalin arziki na kasashen da ke amfani da Euro. Hollande ya kuma tabo dangantaka da ke tsakaninsa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ma dai rashin fahimta dake tasowa tsakaninsu akan wasu muhimman batutuwa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu