Shekaru 20 bayan kisan baki a garin Solingen
May 29, 2013A wannan Larabar a garin Solingen dake yammacin nan Jamus a hukumance aka yi bikin cika shekaru 20 da wani harin da 'yan Nazi masu kyamar baki suka kai kan wani gidan Turkawa. A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1993, matasan Jamusawa masu akidar kyamar baki sun cunna wa gidan iyalin Genc wuta, inda suka halaka yaran mata biyar da kuma mace guda. A shekarar 1995 aka yanke wa wadanda suka aikata wannan laifi hukuncin daurin shekaru da yawa a kurkuku, wanda yanzu haka sun gama zamansa. A jawabin da ta yi a zaman juyayin na wannan Laraba, Mevlüde Genc mahaifiyar yaran mata biyar da aka kashe cewa ta yi.
"Ina tsaye nan a matsayin uwa, ina yi muku jawabi a matsayin uwa, dukkanku kuna da yara da iyaye, idan kun rasa daya daga cikinsu, rayuwarka za ta gurgunce. Na rasa yara biyar. Duniyata ta ruguje gaba daya, ba na jin dadin komai a rayuwata."
Harin dai ya kasance kololuwar jerin hare-haren kyamar baki da suka girgiza Jamus a farkon shekarun gommai na 1990.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman