Jamus da Turkiya na son magance nuna kyama
May 30, 2018Karuwar aikata laifuka da ke da nasaba da kyamar baki da ma illata wasu na cigaba da shan kakkausar suka daga Jamusawa da ma bakin da ke zaune a kasar ta Jamus, duba da yadda yake cigaba da haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin al'umma. Wannan yanayi da ake ciki ne ya sanya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel yin kira da a hada hannu waje guda wajen ganin an kawar da wannan mummunar akida. Kiran na Merkel dai na zuwa ne bayan wani zama na musamman da aka yi domin tunawa da wasu mata 'yan asalin Turkiyya su biyar da aka hallaka a yammacin kasar shekaru 25 da suka gabata ta na mai cewa: "ra'ayi na kin jinin baki abu ne da ba za a ce ya kau ba. Irin wannan halaye abin kunya ne kuma ba za mu taba amincewa da hakan ba idan har muna son mutunta dan Adam kuma kin jinin baki abu ne da ba shi da wurin zama a Tarayyar Jamus."
Wadannan kalamai na Merkel da ma matsayin da ta dauka kan wannan lamari sun faranta ran al'umma musamman ma dai baki da ke zaune a kasar wanda wasunsu ke fuskantar tsangwama daga lokaci zuwa lokaci. Shi ma dai ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu wanda miliyoyin 'yan kasarsa ke zaune a Jamus kuma suke fuskantar matsala ta nuna kyama duk da jimawar da wasunsu suka yi a kasar, maraba ya yi da kalaman na Merkel inda ya ke cewar a shirye suke su dafawa Jamus wajen ganin an kawo karshen wannan matsalar yana mai cewa "matakin Merkel na yakar kyamar baki abu ne da ke kan gaba kuma a matsayinmu na kasar Turkiyya a shirye muke don yin dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an kawar da wariyar launin fata da ma kyamar da ake nunawa Yahudawa."
Wannan tafarki da shugabannin biyu suka dauka dai na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma ke yin kiraye-kiraye na ganin an kawar da banbance-banbance da ke da nasaba da asali da launin fata ko addini ta yadda za a kasance uwa daya uba. Mevlude Genc da ke zaman uwa da aka hallaka yaranta biyu a harin da aka kai na birnin Solingen na yammacin Jamus na daga cikin masu son ganin wannan kalubale ya zama tarihi.