1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: Tasirin mulkin Putin ga Afirka

August 9, 2024

A ranar tara ga watan Agustan shekarar 1999 aka nada Vladimir Putin a matsayin firaministan kasar Rasha, kuma 'yan watanni daga bisani ya zama shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/4jJ5t
Rasha | Vladmir Putin | Shekaru 25 | Madafun Iko
Shugaba Vladmir Putin na RashaHoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

Shugaba Vladimir Putin dai ya mamaye harkokin mulkin Rasha bayan ya zama firaminista a 1999, inda ake ganin irin wannan tasirin a kasashen nahiyar Afirka a yanzu haka saboda kara kusantar kasashe da dama na Afirkan. A lokacin Tsohuwar Tarayyar Soviet dangantaka tsakanin Afirka da Rasha ta takaita ga wasu kasashe kalilan na Kudu da Saharar Afirka da kuma na arewacin Afirka, wadannan kasashen sun hada da Angola da Habasha da Masar da kuma Aljeriya. Sai dai a yanzu lamura sun sauya, inda ake ganin tutocin Rasha na kadawa a wuraren da ake zanga-zanga a yankin Yammacin Afirka.

Karin Bayani: Tasirin Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Masu goyon baya na ganin Rasha a matsayin mai ceto, abin da ke nuni da kara tasirin da ke kara sauya siyasar nahiyar Afirka. Malte Lierl babban mai bincike a Cibiyar Kula da Dangantaka da Kasashen Duniya da ke kasar Netherlands, na ganin da ma Rasha ta dade ana damawa da ita a wannan nahiy. Shugaba Vladimir Putin na Rasha na da hannu, wajen ganin kasarsa ta kara zama mai fada a ji a nahiyar Afirka. Da farko Putin ba shi da wata niyya mai karfi a nahiyar Afirka, inda ya kai ziyara zuwa kasashen arewacin nahiyar da Afirka ta Kudu cikin shekaru 25 da ya kwashe a harkokin mulkin Rashan.

BRICS: Rage tasirin Kasashen Yamma

An samu babban sauyi a shekara ta 2018 lokacin da ya kai ziyara birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, yayin taron kungiyar BRICS. Kuma Shugaba Putin ya bijiro da ra'ayin samar da taron Afirka da Rasha, abin da ya karfafa dangantakar kasarsa da nahiyar. Nan da nan Rasha ta shiga sahun gaba, wajen cinikin makamai da Afirka. A cewar Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya da ke birnin Stockholm fadar gwamnatin kasar Sweden, kimanin kaso 35 cikin 100 na makaman da ke shiga nahiyar Afirka na fitowa ne daga Rasha da ta shiga gaban kasashen Chaina da Amurka. Kana ana kara samun sojojin haya na kamfanin Wagner da ke da alaka da gwamnatin Rasha da ke aiki a nahiyar Afirka, sannan Rasha ta karfafa harkokin diflomasiyya a nahiyar.

Karin Bayani: Ukraine: Kokarin samun wajen zama a Afirka

Har ilya yau Malte Lierl babban mai bincike a Cibiyar Kula da Dangantaka da Kasashen Duniy da ke kasar Netherlands, na ganin Rasha tana amfani da gazawar manufofin kungyiar Tarayyar Turai EU. Tun lokacin Tarayyar Soviet kasar Rasha take amfani da nuna wa 'yan Afirka ita aminiya ce, tare da taimakon kasashen nahiyar wajen kawo karshen mulkin mallaka na kasashen Yamma. Duk da wannan hobbasa ta Rasha kan cinikayyar kimanin dala milyan dubu 17, ba komai ba ce in an kwatanta da ta Chaina ta kimanin dala milyan dubu 200 a shekara. Sai dai ba kowa yake maraba da ingizon Shugaba Vladimir Putin na Rasha a nahiyar ta Afirka ba. wasu kasashen Kudu da Sahara na Afirka da suke dasawa da kasashen Yamma sun nuna damuwa. Misali a arewacin Najeriya lokacin zanga-zanga kan tsadar rayuwa wasu sun fito da tutocin Rasha, abin da rundunar sojan kasar ta yi gargadi a kai tana mai cewa hakan ka iya zama cin amanar kasa.