Shekaru 40 da nasarar juyin juya halin Islama a Iran
A ranar 11 ga watan Farbrairun 1979 Ayatollah Khomeini da magoya bayanshi sun karbi iko a. Doki da murnar kawo karshen gwamnatin Shah ya taimaka Khamenei ya assasa sabon tsarin gudanar da mulkin kasar.
"Bana jin komai"
Khomeini a cikin jirginn saman Air France a kan hanya daga zaman hijira a Paris zuwa Teheran a ranar 1 ga watan Fabrairun 1979. Lokacin da yake amsa tambayar 'yan jarida kan yadda yake ji cewa ya yi "Sam bana ji komai." Wani shauki duk abin duniya ne, shi kuwa Khomeini yana kan hanyar isarsa da sakon Ubangiji ne.
Miliyoyin mutane sun nemi komawar Khomeini gida
A ranaikun 10 da 11 na Disamban 1978 mutane da yawansu ya kama tsakanin miliyan shida zuwa miliyan tara sun yi da maci a manyan birane. Zanga-zangar ta tafi cikin kwanciyar hankali sabanin ta ran 8 ga Satumba, inda aka yi wa mutane kisan gilla a Teheran. Gwamnatin Shah ta gane cewa zamaninta ya wuce, babu kuma abin da zai hana Khomeini karbe ragamar iko.
Su ma mata 'yan Iran ba a barsu a baya wajen neman sauyi
Khomeini tun a zamansa na hijira ya yi ta sukan matakan da Shah ya dauka na ganin mata sun fito an dama da su a fannoni da dama. A shekarar 1963 ga misali an ba wa mata 'yancin yin zabe. Sai dai duk da haka mafi akasarin matan sun shiga jerin masu goyon bayan komawar Khomeini gida da kuma kawo karshen gwamnatin Shah.
Shah a cikin dadadden tarihin Iran
A 1971 Shah da matarsa Farah Diba (hoto) sun dauki hankali a bikiin zagayowar shekara 2500 da kafa Daular Mulukiyyar Iran wuraren kayakin tarihi na Persepolis. Da yawa daga cikin sanannun shugabannin kasar sun halarci bikin. Khomeini ma ya aike da sakon gaisuwa daga ketare, ya yi tir da Daular Mulukiyyar da cewa azzaluma, shaidaniya ba ta kuma kan addinin Musulunci.
A hijira
Tsohon Sarkin Sarakunan Iran Shah Mohammed Reza Pahlavi da matarsa ta uku Farah Diba a hijira a Cuerna Vaca, Mexiko, a watan Yunin 1979. Bisa matsin lamba daga 'yan juyin juya halin Islama a ranar 16 ga watan Janerun 1979 Shah ya bar kasar Iran. Bayan kai komo a kasashe da dama da jinya daga wannan asibiti zuwa wancan, a ranar 27 ga watan Yulin 1980 Shah ya rasu a Kairo sakamakon cutar daji.
Abubuwa mabambanta da farko
Masu sanya hijabi ko wadanda ba sa sanya hijabin, da farko dai juyin juya halin ba mayar da hankali kai ba. Bayan samun nasarar juyin juya halin aka assasa sanya tufafi bisa shari'ar Musulunci.
Sojoji sun bi sahun juyin juya hali
'Yan uwantaka tsakanin sojojin da fararen hular Iran a watan Janerun 1979 a Teheran babban birnin kasar. Sojojin sun daga jajayen furanni da ke zama alamar zaman lafiya. A 11 ga watan Fabrairu sojojin sun ayyana matsayinsu na 'yan ba ruwanmu. Duk da haka a watannin Fabrairu da Afrilu an aiwatar da hukuncin kisa kan janar-janar da dama bayan hukuncin kotun juyin juya hali.
Jawabi ga 'yan kasa daga babbar makabarta
Da komarsa Khomeini ya ayyana Daular Mulukiyya da gwamnati da majalisar dokoki da cewa sun haramta, inda ya ce: "Zan nada wata gwamnati saboda yardar da kasar nan ta nuna mini." Masana harkokin kasar sun bayyana kalaman a farkon shekarar 1979 da cewa ba yaudara ba ce, gaskiya ce kuma zahiri.
Masu sassaucin ra'ayi na juyin juya hali
Mehdi Bazargan (1908-1995) tun a shekarun 1930 yake adawa da mulkin mulukiyya na gidan Pahlavi, abin da ya jawo mishi daurin shekaru da yawa a kurkuku. Khomeini ya nada shi a mukamin Firaministansa na farko, duk da sukan da Bazargan yake mi shi. Ya ce ya ga "Shah da rawani", bayan wata ganawa da ya yi da Ayatollah a birnin Paris. Wata tara ya yi kan mukaminsa.
Mamaye ofishin jakadancin Amirka ya karfafa matsayin Khomeini
A Nuwamban 1979 dalibai masu ra'ayin rikau sun mamaye ofishin jakadancin Amirka a Teheran sun kuma yi garkuwa da ma'aikatan jakadancin. Dalili shi ne fargabar cewa Amirka ka iya taimaka wa Shah ya koma gida. Khomeini ya yi amfani da goyon bayan da juyin juya halin ya samu: An kame masu sukar daftarin tsarin mulkin da ya ba shi matsayin babban jagoran addini, da cewa kawayen Amirka ne.
Ali Khamenei - Mai kare tsarin da ya cije
A 1989 majalisar masana ta zabi Ali Khamenei a mukamin magajin Khomeini. Har yau shi ne babban jagoran addini da malamai a dukkan cibiyoyi na gwamnati. Dan shekaru 79 a yanzu ba shi da kwarjini irin na magabacinshi. Yana bi sau da kafa manufofin masu ra'ayin rikau da ke adawa duk wani matakin kawo sauyi a tsarin mulkin kasar suna kuma daukar matakan rashin imani kan masu adawa.