Shekaru 50 da harin Olympics na birnin Munich
Wasannin Olympics na 1972 a Munich: 'Yan ta'addar Falasdinu sun yi garkuwa da mutane 11 na tawagar Olympics ta Isra'ila. Yunkurin kubutar da jama'a ya kare cikin zubar da jini.
Wasanni masu annashuwa
Birnin Munich a matsayin mai masaukin baki na gasar Olympics ta 1972 ya kasance wata cibiya ta haduwar al'adu dabam-dabam. Wasan ya kamata ya kasance fiye da na wasannin Nazi na 1936 a Berlin. 'Yan sandan yankin ba su cikin kaki kuma ba su dauke da makamai, sun kasance a bayan fage. Kwanaki 10, Munich na bikin cikin lumana tare da baki daga ko'ina cikin duniya.
Babban abin yabawa
Dan wasan ninkaya na Amirka Mark Spitz ya lashe zinare sau bakwai. Daga bangaren Jamus, 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle sun yi rawar gani: Heide Rosendahl ta lashe zinare a wasan tsallen kasa da kuma tseren gudun ba da sanda, Klaus Wolfermann a jifar mashi. Ulrike Meyfarth mai shekaru 16 kawai wadda hotonta ke a sama ta zama zakaran gasar Olympics a babban tsalle na sanda.
Harin safiya
Mambobi takwas na kungiyar 'yan ta'addar Falasdinu "Black Satumba" sun shiga wani gida na tawagar Isra'ila a masaukin 'yan wasan a daren 5 ga watan Satumba 1972. Sun harbe kocin wasan kokawa Mosche Weinberg tare da raunata dan wasan daukar nauyi Josef Romano, yayin da wasu tara da aka yi garkuwa da su suka zauna a daure a daki daya suna kallon yadda ya mutu.
Tattaunawar da ba ta yi nasara ba
'Yan ta'addar na neman a sako fursunoni sama da 200 daga hannun Isra'ila. Don haka, suna son su saki mutanen da suka yi garkuwa da su idan har za a saki nasu, idan ba haka ba su kashesu. Ministan harkokin cikin gida na tarayya Hans-Dietrich Genscher (na uku daga hagu) da wasu jami'ai suna tattaunawa da shugaban 'yan ta'addar, wanda ya kira kansa Issa.
Isra'ila ta aiwatar da karfin ikonta
"Idan muka ba da kai, babu wani Ba'isra'ile a duniya da zai sake samun tabbas a kan rayurwasa", Firaministar Isra'ila Golda Meir ta yi watsi da tayin. Amma Isra'ila ta yi tayin tura dakaru na musamman domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su. Gwamnatin Jamus ba ta ba da hadin kai ba, watakila saboda doka da ta hana tura sojojin kasashen waje a Jamus.
Dakatar da wasan a kan matsin lamba
Duk da kashe-kashen da aka yi da kuma yin garkuwa da mutane an ci gaba da yin gasar. Yayin da jami'an 'yan sanda suka killace gidan da 'yan ta'addar suka mamaye, 'yan kallo sun yi cincirindo a filin wasannin na Olympics. Sai da masu zanga-zangar nuna goyon baya ga Isra'ila suka bukaci a dakatar da wasannin aka ba da umarnin dakatar da gasar a yammacin ranar 5 ga Satumba.
Kai hari kai tsaye a talabijin
'Yan sandan Bavaria ba su da shiri sosai domin fuskantar wannan lamarin kuma ba a horar da su don irin wannan aiki ba. Jami'an 'yan sanda dauke da makamai sun yi kokarin kutsawa cikin gidan da ke titin Connolly 31, amma ba a gane su ba. An rika yada shirye-shiryen talabijin kai tsaye yadda jami'an suke tunkarar masu garkuwa da mutane. 'Yan ta'addar ma suna ganin haka amma daga baya an dakatar..
Amintaccen hali, mai kama da tarko
'Yan ta'addar sun kara wa'adin sau da yawa. A karshe dai an amince cewa jirage masu saukar ungulu guda biyu za su kai su filin tashi da saukar jiragen sama na soja na Fürstenfeldbruck, kuma za a kai su birnin Alkahira, tare da wadanda suka yi garkuwa da su. Sai dai ga alamu masu shiga tsakani na Jamus suna amsa bukatun ne kawai. Suna son shirya tarko ga 'yan ta'addar amma lamarin ya kare ba kyau.
Rashin shiri
Wani jirgin Boeing yana jira a filin jirgin sama na Fürstenfeldbruck, tare da jami'an 'yan sanda wadanda suka yi shigar burtu da kayan matuka jirgin ma'aikatan. Amma jami'an ba su da isassun makamai ko horo don wannan aikin. Dubarar ba ta ci ba. 'Yan sandan da ke a filin jirgin saman ba su san cewa ba masu yin garkuwa da jama'ar su takwas ne a maimakon biyar ba.
An zubar da jini
Yayin da wasu 'yan ta'adda biyu ke duba jirgin Boeing, 'yan sanda sun bude wuta. An kwashe sa'o'i ana gwabza fada. An samu karfafawa a makare. A karshe 'yan ta'addar sun tarwatsa daya daga cikin jirage masu saukar ungulu da gurneti, inda suka harbe fursunonin. A karshe, mutane 15 ne suka mutu, dan sanda daya, biyar daga cikin wadanda suka yi kisan gilla da kuma wadanda aka yi garkuwa da su tara.
"Dole ne a ci gaba da wasannin"
An gudanar da taron tunawa da wadanda aka kashe a filin wasa na Olympics a ranar 6 ga watan Satumba. A sama, Shugaban IOC Avery Brundage ya ba da sanarwar cewa ba za a ba da kai bori ya hau ba ga ta'addanci. "Dole ne a ci gaba da wasannin''. Duk da haka, wasannin na Munich ba su yi armashi ba a sauran kwanakin da suka biyo baya.