1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 na huldar Isra'ila da Jamus

Yusuf BalaFebruary 16, 2016

A bara ne dai mahukuntan birnin Berlin suka tsara tattaunawa da ma shirya wani biki na tunawa da shekaru 50 na kulla dangantaka ta diplomasiya tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/1HvzQ
Bundeskanzlerin Merkel trifft Israels Premierminister Netanjahu in Berlin
Firaminista Netanyahu da shugaba MerkelHoto: Reuters/BPA/G. Bergmann

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tsara ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar Talatan nan, a ziyarar da ke zuwa watanni hudu bayan lokacin da aka shirya yinta sai dai an samu tsaiko saboda rudanin da Isra'ila ta shiga.

A shekarar bara ne dai mahukuntan na birnin Berlin suka tsara tattaunawa da ma shirya wani biki na tunawa da shekaru 50 na kulla dangantaka ta diplomasiya tsakanin kasashen biyu.

Isara'ila da Jamus dai na da burin fidda tsari na tunkarar kalubalen aikata miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo da ma hada kai wajen samar da wasu ayyuka na ci gaba a nahiyar Afirka. Wannan dai ana gani wata dama ce da Mista Netanyahu zai yi amfani da ita dan tattaunawa da mahukuntan na Berlin kan abin da ya dade yana sosa masa rai wato dangantaka tsakanin manyan kasashen duniya da kasar Iran, kasashen kuma da kasar ta Jamus na cikinsu.