1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 na jimamin kisan 'yan wasan Olympics a Munich

September 5, 2022

Shugaban kasar Jamus Walter Steinmeier a ya nemi afuwa kan gazawar kasar na kare 'yan wasan Israila da tawagarsu wadanda aka yi wa kisan gilla shekaru 50 da suka wuce a lokacin wasannin Olympics a 1972 a birnin Munich.

https://p.dw.com/p/4GRyg
Gedenkveranstaltung zum 50. Jahrestag des Olympiaattentats
Hoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

Steinmeier ya shaida wa taron jama'ar da suka hallara a wurin bikin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu da suka hada da dangin mamatan da kuma jami'an Israila cewa babu yadda za a halasta abin da ya faru.

 "Ya ce sai fa idan mun fahimci gaskiya kuma mun yarda da kura kurai da gazawarmu sannan za mu iya warkar da wannan ciwon wanda mu da kasarmu muka sha fama da shi tun 1972" 

Falasdinawa 'yan kungiyar da ake kira Black September suka yi garkuwa da 'yan wasan Olympic na Israila a ranar 5 ga watan Satumbar 1972.

Yan Israila goma sha daya da dan sandan Jamus daya da kuma Falasdinawa biyar 'yan bindiga suka rasa rayukansu yayin harin a tsangayar wasannin na Olympics.