Shekaru 60 da gina katangar Berlin
August 13, 2021A wannan ranar dai kusan dukkanin tashoshin shiga motocin bas a tsakanin gabashi da yammacin Berlin sun kasance a rufe. Jamus ta Gabas karkashin mulkin kwaminisanci ta tura dakarunta duk suka yi shinge a kan iyakarsu da yammacin Berlin.
Akalla dai mutane 140 ne suka mutu cikin shekaru 28 da aka yi ana aiki da katangar ta Berlin a matsayin maraba tsakanin Jamus. Katangar mai tsawon mita 200, a lokacin wasu Jamusawan sun yi ta zuwa kusa da ita domin kashe kwarkwatar ido. Sai dai wasu kam sun gamu da mummunan abin da har iya rayuwa zai ci gaba da zama a kwakwalwarsu.
Sai dai ko da a bayan sake hadewar Jamus kasa daya, kusan duk inda Bajamushe yake a duniya ba abin da yake yi illa fadakar da ‘ya’yansa halin da kasarsu ta kasance, kamar yadda ta faru da Lena Quincke ‘yar shekaru 22 wacce aka haifa a kasar Kamaru kuma ta girma a Habasha, kafin ta koma Jamus inda ta karanci ilimin shari’a.
Ta ce duk da cewa a Afirka na da girma, amma tun da tana halartar makarantun alfaramar na kasashen waje, kusan ba abin da ake yi kamar labarin katangar Berlin.
Sai dai fa wasu a cikin kasar ta Jamus sai labari suke ji, ko da kuwa suna cikin birnin Berlin, sai dai sun kai ziyara. In ba wadanda ke zama kusa da inda aka gina katangar ba.
Yayin da Jamus ta Gabas ke karkashin ikon Rasha, ita kuwa Jamus ta Yamma ta kasance a layin Amirkawa. A wancan lokaci har zuwa 1989 da aka rusa katangar, an yi ta gudun hatsarin sake barkewar yakin duniya na uku. To amma an kauce masa.
Sai dai kuma har yanzu akwai masu ra’ayin irin wannan batu na raba kasashe ta hanyar gina katanga, kamar yadda aka gani a mulkin tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump, wanda ya gina katanga mai tsawo tsakanin kasar da Mexiko.