1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 da sa hannu kan yarjejeniyar birnin Rome

Salissou Boukari
March 24, 2017

Tunawa da zagayowar ranar cika shekaru 60 da saka hannu kan yarjejeniyar birnin Rome na Italiya wadda ta zama sassalar samun kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/2ZtU3
EU Ratspräsidentschaft Malta
Zauran muhawara na shugabannin Tarayyar TuraiHoto: Pressestelle Europäischer Rat, Malta

Kare sake samun yakin ya kasance a zuciyar shugabannin kasashe shida da suka kulla yarjejeniyar ta birnin Rome. Shugaban gwamnatin Jamus na lokacin Konrad Adenauer ya yi jawabin nuna muhimmancin hadewar kasashen Turai. Kasashen shida da suka kulla yarjejeniyar sun hada da: Beljiyam, Jamus, Faransa, Italiya, Holland, da kuma Luxemburg, inda Jamus ta mamaye kasashe biyar daga ciki lokacin yakin duniya na biyu. 'Yan siyasa da suka jagoranci kulla yarjejeniyar suna da kwarewa kan abin da 'yan Nazi na Jamus suka aikata, a cewar Lutz Klinkhammer mataimakin daraktan cibiyar tarihin Jamus da ke birnin Rome na Italiya wannan shi ne makasudin bin irin wannan tafarki:

An saka hannu bayan yakin duniya na biyu

Lutz Klinkhammer, Historiker am Deutschen Historischen Institut in Rom
Lutz Klinkhammer mataimakin daraktan cibiyar tarihin Jamus da ke birnin Rome na ItaliyaHoto: DW/B. Riegert

"lokacin bayan kammala yakin duniya na biyu da shekaru 12, a shekarar 1957. Yakin yana cikin kwakwalwar mutane ba su gama warwarewa ba, lokacin ake tutanin kare sake samun wani yakin a gaba, ake neman kirkiro hanyoyin zaman lafiya musamman tsakanin kasashen Jamus da Faransa, abin da ya zama mafarin yarjejeniyar birnin Rome wadda aka saka hannu a kanta a ranar 25 ga watan Maris na 1957."

yakin cacar-baka ya kunno kai tsakanin kasashen gabashi da yammacin duniya, kana kasashen Turai sun shiga rudani bayan yakin duniya na biyu, wadannan sun yi tasiri kan inda aka nufa a cewar Angelo Bolaffi masanin harkokin siyasa na Italiya:

Yarjejeniyar birnin Rome ta kumshi abubuwa da dama

Angelo Bolaffi, Politikwissenschaftler Portrait
Angelo Bolaffi masanin harkokin siyasa na kasar ItaliyaHoto: Ilja Luciani

"Duk wannan an yi tare da karfafawa, lokacin yakin cacar-baka, da barazana da ake gani daga Rasha, da matsin lamba da hakan ya haifar, kamar yadda ake gani da Trump a wannan lokaci. Tsoron abin da ka iya faruwa ya saka kasashen kusanta da juna maimakon samun matsala. Haka yarjejeniyar Rome ta zama cibiyar ruhin siyasa na kasashen Turai."

Ba ruhin siyasa kadai ba, an samu wata hanyar warare matsalolin tattalin arziki cikin kasashen Turai wajen zirga-zirgar kayayyaki da mutane ba tare da wani shinge ba, abin da ya janyo hankalin wasu kasashe suka shiga cikin kungiyar. Wannan ya janyo sake wasu yarjiniyoyin a biranen Maastricht na Holland da Lisbon na Portugal a cewar masanin tarihi Lutz Klinkhammer:

Taron saka hannu kan yarjejeniyar birnin Roma

Jahrestag 50 Jahre Römische Verträge
Zaman taron saka hannu kan yarjejeniyar birnin Rome ranar 25 ga watan Maris 1957.Hoto: AP

"Tunanin shi ne kirkiro zaman lafiya ta hanyar hadakar kasuwanci da bunkasa. Kuma ta haka ne a hannu daya za a kirkiri cinikyayya da yelwata a lokaci daya za a kare sake samun wani yaki nan gaba wanda ya zama abin da zai iya jan hankali."

Tarayyar Soviet ta rushe tare da kawo karshen yakin cacar-baka, tunanin yakin duniya na biyu ya gushe ga matsaloli na tattalin arziki, lamuran da suka zama barazana kan shirin Turai, inda shekaru 60 bayan kafa wannan shiri, duk abubuwa da za su faru nan gaba ke tantance makomar wannan tsari.