1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 65 da barkewar yakin duniya na biyu

Mohammad Nasiru AwalSeptember 1, 2004
https://p.dw.com/p/Bvgp
Adolf Hitler a shekarar 1937
Adolf Hitler a shekarar 1937Hoto: AP

Jawabin da Adolf Hitler yayi kenan a ran daya ga watan satumban shekara ta 1939, lokacin da dakaraun Jamus suka kutsa cikin kasar Poland. A jajiberen wannan rana kuwa sojojin rundunar SS ta Jamus sanye da kayan dakarun Poland sun mamaye tashar radiyon Jamus dake yankin Gleiwitz. Hitler yayi amfani da wannan damar a matsayin hujjar kaddamar da yaki akan Poland.

Shi dai Hitler ya dade yana begen hakan ta faru. Domin tun a shekaru 15 baya, a cikin litttafinsa mai taken Gwagwarmaya Ta, Hitler yayi nuni da cewa kamata yayi Jamusawa su kwace wasu yankuna da bakin bindiga, domin a nasa ra´ayin sai mai karfi ka iya rayuwa.

Tun a zamanin janhuriyar Weimer dangantaka tsakanin Jamus da Poland ta yi tsami sakamkon yarjejeniyar zaman lafiya ta Versail a 1919, wadda ta tanadi mayarwa Poland wasu yankunanta, musamman na gabashin yankin Purusiya. Babu wani dan siyasar Jamus da ya amince da haka. A saboda haka a lokacin da Hitler ya dare kan karagar mulkin a shekarar 1933, yayi ta kokarin kusanta da Poland. Sannan don tabbatar da cewa da gaske yake, a shekarar 1934 an kulla yarjejeniyar hana kaiwa juna hari tsakanin Poland da Jamus. A fili dai Hitler ya nuna shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu, inda a cikin wani jawabinsa yayi watsi da daukar matakan soji akan Poland.

"Babban kuskure ne a yi amfani da yaki don warware bambamce-bambamce tsakanin kasashen biyu. Saboda haka gwamnatin Jamus na farin ciki game da cewa shugaban Poland na yanzu Marshall Pilsudski ya san da haka, kuma yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla zata amfanar da al´umomin Poland da Jamus tare da ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya gaba daya."

To sai dai a hakikanin gaskiya, Hitler ba mai son zaman lafiya ba ne, domin ya ci-gaba da aiwatar da shirinsa na fadada yankunan Jamus, inda a shekarar 1938 ya mayar da kasashen Austriya da Czechoslovakiya karkashin inuwar daular Jamus.

Ita kuwa Poland ta shiga sahu ne sakamakon wata yarjejeniyar zaman lafiya da Hitler da Stalin suka sanyawa hannu a karshen watan agustan shekarar 1939, wadda a ciki Jamus da TS suka shirya raba Poland tsakaninsu. Mako guda bayan haka dakarun Jamus suka mamaye Poland. Ko da yake shugabannin Poland sun san da shirye-shiryen da Jamus ke yi na faka musu da yaki, amma sun yi mamakin wannan kutsen. Da sanyin safiyar ranar daya ga watan satumban 1939 sojojin ruwa Jamus suka fara kai farmaki akan birnin Danzig. Sannan sa´o´i kalilan bayan haka Hitler ya bayyana a gaban majalisar Reichstag yana mai cewa:

"Duk wanda ya nesanta kanshi daga bin dokokin yaki, to dole ya tsammaci irin wannan mataki daga bangarenmu. Zan ci gaba da wannan yaki akan ko-wane ne kuwa har sai na tabbatar da tsaron lafiya da kuma ´yancin daular Jamus."

Kwanaki biyu bayan haka, Ingila da Faransa suka kaddamar da yaki akan Jamus, abin da ya janyo barkewar yakin duniya na biyu.