Shekaru 70 bayan kulla yarjejeniyar Geneva Convention
August 12, 2019Yayin da yarjejeniyar nan ta kasashen duniya kan kare hakkin bil Adama lokacin yaki ke cika shekaru 70 cif bayan yakin duniya na biyu, kungiyoyin agaji na duniya na bayyana ra’ayoyi game da ko ana bin dokokin da ke cikinta a yau ko kuma akasin hakan. Kasashen duniya dari da casa'in da shida ne dai suka yarda cewar tilas, a mutunta hakkin jama’a walau fararen hula ne ko jami’an agaji da na kiwon lafiya gami da sojoji a lokutan yaki.
Sabbin hare-haren kan gidajen jama’a a Siriya da kuma hare-haren jiragen yaki kan asibitoci a Yemen sai kuma daruruwan da ake kashewa a Afghanistan a bana, shekaru 70 bayan amincewa da yarjejeniyar ta Geneva Convention, kan kare hakkin bani Adama daga rashin imani a yaki, kungiyar agaji ta Red Cross na cewa ba su da wani tasiri. Babban daraktan kungiyar, Kenneth Roth, ya ce akwai misalai da daman a take hakkin mutane da aka gani, kama daga kasar Myanmar zuwa Yemen da ma Siriya. Amma akwai wata a kungiyar ta Red Cross da ke da ra’ayin cewar, duk da gani da ake yi ana saba wa yarjejeniyar, hakan baya nufin ba su da wani tasiri ba inji Helen Durham, mai jagorantar bangaren dokoki na kungiyar.
Cikin wani jawabin da yayi a baya-bayan nan shugaban hukumar bayar da agaji ta Int’l Committee of the Red Cross, Peter Maurer, ya ce a wurare kalilan ne ake bin dokokin da kasashen suka tsara, na kare hakkin jama’a a wuraren yakin, wanda ke cika shekaru 70, idan aka kwatantat da dubban wuraren da ake karya ka'idojinsu. A cewarsa idan ana ganin kananan yara na samun abinci da sauran bukata ta kulawa, ko kuma ana ba da damar wucewa ga wadanda aka ji wa rauni a shingayen bincike don samun magani, babu wanda zai kalubalanci hakan.