1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwar Holodomor ta cika shekaru 90 a Ukraine

November 26, 2022

Holodomor dai yunwa ce da dan Adam ya kirkira a tsohuwar kasar Ukraine karkashin rusasshiyar Tarayyar Soviet a tsakanin shekarun 1932 zuwa 1933, lamarin da ya yi ajalin miliyoyin mutanen Ukraine.

https://p.dw.com/p/4K8Sp
BdTD Kiew Gedenken an Opfer Hungersnot in Sowjet-Ära
Hoto: GENYA SAVILOV/AFP

A yayin da a Asabar din nan Ukraine ke bikin tunawa da ''yunwar Holodomor'' wacce ta halaka miliyoyin 'yan kasar a shekaru 90 da suka gabata, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wajibi ne a dauki matakin hana yunwa zama wani makami a rikicin da Ukraine ke yi da Rasha. 

Scholz wanda ya halarci bikin na Holodomor a Ukraine tare da wasu shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai, ya ce, duk da kulla yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine, Rasha na ci gaba da mayar da hannun agogo baya, inda take kai hare-hare kan kamfanonin da ke harkar noma. Ya ce wannan mataki da Rasha ke dauka ne ya haddasa karanci tare da tsadar kayan abinci a duniya.