Shekaru biyar da girgizar kasa a Haiti
January 12, 2015A wannan Litinin ne ake cika shekaru biyar da faruwar bala'in girgizar kasa mai karfi maki bakwai da ta girgiza kasar Haiti a ranar 12 ga watan Janairu na shekarar 2010. Sama da mutane 300,000 suka rasu yayin da kimanin miliyan daya da rabi suka rasa muhallansu.
Duk da cewa an sami ci gaba wajen farfado da yankunan da girgizar tafi muni a cikinsu, amma kuma cewar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon har yanzu wannan kasa na bukatar tallafi na kasashen duniya.
Wannan na zuwa ne a daidai likacin da shugabanni da 'yan majalisa na bangaren adawa na Haiti suka shiga wata tattaunawa don ganin an samu bakin zaren warware rikici da ya dabaibaye siyasar kasar. Shugaba Michel Martelly ya shiga takun saka da 'yan majalisa kan zaben 'yan majalisa da ya kamata a yi shi tun shekarar 2011.