1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Shekaru biyar na mulkin Paparoma Francis

March 13, 2018

Shugaban darikar Katolika ta addinin Kirista Paparoma Francis ya cika shekaru biyar da karbar jagorancin darika a duniya bayan da wanda ya gada ya yi murabus.

https://p.dw.com/p/2uErc
Papst Franziskus
Hoto: picture-alliance/Catholic Press Photo

Gudanar da addu'a ka iya zama siyasa, musamman idan a tsakanin kasashen Amirka da Mexiko da ake maganar kara shinge iyaka tsakanin kasashen biyu. Sai dai Paparoma Francis ba ya shakka, inda ya ce duk mutumin da yake tunanin gina katanga tsakanin mutane maimakon gina gada, ba ya bin tafarkin addinin Kirista, abin da karara yake yi da Shugaba Donald Trump na Amirka, wanda ya tsaya kai da fata sai ya dillace iyakar kasar da Mexiko. Shi dai Paparoma ya yi kalaman shekaru biyu da suka gabata lokacin ziyara a Mexiko. Daga bisani Shugaba Trump na Amirka ya kai ziyara fadar Vatikan inda ya gana da Paparoman duk da sabanin da ke tsakanin mutanen biyu.

Mexiko Papst in Ciudad Juarez
Hoto: Getty Images/AFP/R. Schemidt

Bernd Klaschka tsohon babban jami'in bayar da taimako a yankin Latin Amirka yana gani Paparoman ya taka rawar gani. Bernd Klaschka ya kara da cewa haka labarin ya ke a kasar Kuba wajen inganta dangantaka da Amirka. Shi dai Jorge Bergoglio dan shekaru 81 daga Argentina ya kwashe shekaru biyar kan kujerar Paparoma. Mintoci biyu kacal bayan zabensa ranar 13 ga watan Maris na shekara ta 2013, sabon Paparoma da ya fito daga wani bangare na duniya ya nuna ya na da banbanci da sauran magabata.

Peru Trujillo - Papst zu Besuch
Hoto: picture-alliance/dpa/Agentur Andina/J. C. Guzmán

Rikice-rikice kamar na nahiyar Afirka na cikin batutuwa da Paparoma ya ke magana a kai inda ya kai ziyara Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula kamar yadda Dieudonne Nzapalainga Arcbishop na birnin Bangui fadar gwamnatin kasar ya tabbatar. Tun lokacin da Paparoman ya dauki madafun ikon ya kai ziyara kasashe da suka hada da inda ya fito na Latin Amirka.