Guinea Conakry: Shekaru biyun mulkin soja
September 6, 2023A ranar biyar ga watan Satumbar shekara ta 2021, al'umma a kasar Guinea Conakry suka wayi gari da juyin mulkin da ya yi awon gaba da gwamnatin Shugaba Alpha Conde. To sai dai shekaru biyu bayan nan, sojojin sun bayyana samun nasorori a fannoni da dama, yayin da a nasu bangaren jam'iyyun adawa da ke zargin sojojin da cin-hanci da rashawa na kuka kan yadda suka ce suna jan akalar shugabancin kasar. Jam'iyyun adawar sun musanta samun nasara da sojojin ke ikirarin yi wajen saisaita al'amuran kasar, hasalima sun ce ba a taba samun gwamnatin da ta mayar da kasar baya ba kamar wannan ta Kanal Mamady Doumbouya. Jam'iyyun adawa da kungiyoyin masu zama kansu sun yi amfani da zagayowar ranar juyin mulki wajen yin kira ga magoya bayansu da su fito zanga-zangar lumana, domin nuna adawarsu a kan yadda sojojin ke tafiyar da mulki a kasar.
To sai dai sojojin sun haramta wannan boren, inda wasu matasa da suka ki bin umurnin suka hadu da fushinsu da har aka sami salwantar rayuka da jikkatar wasu. Titunan yankunan Guinea Conakry da 'yan adawa ke da rinjaye sun yi fayau kowa ya kasance a gida, inda jami'an tsaro dauke da manyan bindigogi ke kara-kaina a manya da kananan titunan yankin yayin da wasu ke cewar sun jiyo amon harbin bindiga daga gidajensu. Fayimba Mara da ke sharhi a kan lamuran siyasa a kasar ya ce, magance matsalolin siyasar kasar na a hannun sojoji ne. Rashin cimma kwakwarar matsaya a tsakanin sojoji da 'yan adawa da a kullum lamarin ke kara tsami, wanda kuma al'ummar kasar ne ke kwana a ciki. Da dama daga cikin al'ummar Guinea Conakry ba sa maraba da gwamnatin sojojin kan tsananin talauci da suka ce sun jefa su a ciki. Guinea Conakry na cikin jariran kasashe hudu rainon Faransa da aka aiwatar da juyin mulki, a cikin shekaru uku na baya-bayan nan.