Shekarun da bin Laden ya shafe a Pakistan
May 7, 2011Ɗaya daga cikin matan marigayi Osama bin Laden ta bayyana cewar maigidanta da sojojin Amirka suka kashe ya shafe shekaru biyar yana rayuwa da iyalinsa a gidansa na Abbotabad da ke kusa da birnin Isalamabd na Pakistan. Jami'an tsaron wannan ƙasa suka ce mai ɗakin bin Laden da ta fito daga Yemen, wacce ta ji rauni a lokacin kwantar bauna na ɗaya ga watan mayu, da ma dai kuma wasu matasan biyu da kuma 'ya'yan bin Laden 13, suna samun kulawar da ta dace a fannin kiwon lafiya, tare da amsa tambayoyin kan rayuwar bin laden da kuma manufofin ƙungiyarsa ta Al-Qa'ida.
Hukumomin Amirka suka ce suna nazarin waɗansu bayanan da suka gano a gidan bin laden bayan an kashe shi, waɗanda suka haɗa da nau'rorin kwamfuta da faya fayan CD. Manyan jami'an gwamnatin Barack Obama sun bayyana cewar ƙungiyar Al-Qa'ida na shirin kai hari akan jiragen ƙasarsu a ranar bikin cika shekaru goma da harin nan na sha ɗaya ga watan Satumba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala