Shekau ya ce ba a raunata shi ba
September 25, 2016Jagoran kungiyar Boko Haram a sabon faifan bidiyo inda ya ke nuna cewa ya na nan a raye. Wadanda suka saba ganin sakon da kungiyar ke fitarwa dai sun tabbatar da cewa wanda ya fito a wannan faifan bidiyo jagoran kungiyar ne Abubakar Shekau. Sabon bidiyon mai tsawon mintuna 38 wanda aka sanya a shafin Youtube ya nuna Shekau a zaune da bindiga a kan cinyarsa da wasu litattafai a gabansa tare da wasu kwamandoji guda biyu a tsaye dauke da makamai.
Shugaban ya yi jawabi mai tsawo cikin harshen Larabci kafin daga bisani ya koma harshen Hausa da Fulatanci da kuma Kanuri, inda ya sake jaddada matsayin kungiyar na cewa ba za su sako ‘yan matan Chibok ba sai an sako musu ‘yan uwan su. A cikin jawabin nasa ya kuma kare matsayin kungiyar kan zargin da ake musu na hallaka bayin Allah inda ya bada hujjoji daga cikin litattafai. To sai dai fitowar wannan sabon faifan bidiyo a wannan lokaci zai bude shafin muhawara kan irin bayanai da gwamnati ko jami'an tsaro ke bayarwa a kan hakikanin abinda ke faruwa a yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya. Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba game da wannan sabon bidiyon da Boko Haram din ta fidda.