Shin Beraye abin kyama ne ko kuwa ban sha’awa?
25 ga watan Janairu ce ranar da shekarar Beraye ta fara. A hasashen Chaina, suna wakiltar hikima da farin ciki da sa'a- a yankin yammaci na Turai kuwa ana dangantasu da cuta kuma abin kyama.
Dakon wannan shekara ta beraye
A tarihin hasashen masana dabbobi na kasar Chaina, sun danganta ninkuwar adadin beraye a matsayin alamu na bunkasar tattalin arziki da yalwatuwar dukiya. Dabbar na wakiltar jajircewa da hankali, daura da ban mamaki, wanda ke nuni da cewar 2020 za ta kasance shekara mai riba. Musamman idan za ka saye gida ko bude kamfani ko kuma shiga harkar kasuwanci.
Beraye na kalaci
Wajen beraye dubu 20 ke rayuwa a wurin bauta na Karni-Mata a yankin Rajasthan na arewacin Indiya. Tarihi na nuni da cewar, berayen na zama fatalwa da ke karkashin kariyar abin hidima Durga. Ko abar bauta Ganesha na hawan beraye, wanda ke nufin basira da karfi. Idan bera ya bi kan kafar mutum a wurin bauta na Karni-Mata, mai shi ya yi babbar sa'a.
Bera ya yi fice wajen bincike
Akwai nau'o'i na beraye wajen 65, yawancinsu na zaune a cikin gandun daji. Berayen sun samo asali ne daga yankin Kudu maso Gabashin Asiya, kafin suka bazu zuwa Indiya da Chaina ta kan tsibirin Indonesiya har zuwa New Gini da Oustraliya. Sakamakon harkokin bil Adama da suka hada da gudu cikin dusar kankara, ya sa berayen gida suka bazu zuwa sassan duniya, ciki har da nahiyar Turai.
Beraye na da kazanta
A takardun addini kamar Torah na Yahudawa da Bible na Kiristoci da Kur'ani na Musulmi dai, beraye ba sa taka wata muhimmiyar rawa. Sai dai berayen da suka shigo Turai, ba abincin mutane kawai suke cinyewa ba, har da yada kwayoyin cuta, kasancewar suna rayuwa ne a wuraren kazanta kamar juji da magudanan ruwa masu kazanta.
Al'adar kazantar beraye
Dubban masu yawon bude ido ne ke zuwa Hameln a kowace shekara, domin ganin tarihin fitaccen matashin nan mai busa sarewa da ya kori beraye. Tarihi na nuni da cewar, a shekara ta 1284, ya 'yanta birnin arewacin Jamus daga annobar beraye ta hanyar dauke hankalinsu da sarewarsa. A yau ana amfani da abubuwa kamar tarko da guba da ke sanya dabbobin mutuwa ta hanyar zubar jini.
Beraye a matsayin dabbobin gida
Wasu na mayar da beraye dabbobin cikin gida, musammam masu tsabta daga cikinsu. Duk da yadda ake musu kallon nau'in masu kazanta, wasu berayen na da tsabta, bisa la'akari da inda suke rayuwa. Yawancinsu na da launuka dabam-dabam da kuma yawan gashi.
Beraye sun iya zamantakewa kuma ga basira
Beraye na rayuwa ne tare a matsayin iyali, sun san 'yan uwan junansu ta hanyar sunsuna. Domin tabbatar da ci-gaban kowace al'umma, a kan bar kanana da marasa galihun cikinsu cin abinci da farko, kafin manya masu jini a jika. Beraye na da basirar gane wuri, kuma babu wuya su saba da kewayensu.
Beraye a matsayin abin gwaji
Saboda yanayin yadda halittarsu take, a kan yi gwaji da beraye, saboda ba su da saurin fushi kamar karnuka da birai. Kasancewar suna saurin haihuwa kuma kulawa da su na da sauki babu tsada, bera ne abu mafi sauki wajen gwaji. A nan Jamus kadai, an kiyasta amfani da beraye wajen dubu 500 wajen yin gwaji a asibitoci a kowace shekara.
Beraye na iya gane warin abubuwa masu fashewa
Karnuka ku yi hattara: Yanzu kun samu abokan gasa ta basirar shinshina da hanci. Wasu nau'o'in beraye na da basirar jin warin abu fiye da fitattun karnuka da ake amfani da su a nan Jamus. Idan sun jiyo warin abubuwa masu fashewa za su tsaya cik a wurin. Ga misali da taimakon beraye ake binciken nakiyoyin karkashin kasa a Thailand da Angola da Kambodiya da kuma Mozambik.