Shin zanga-zanga a Iran za ta kare
February 15, 2011Bayan zanga- zangar da aka yi jiya a kasar Iran, wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar, sun yi kira da ayi wa shugabannin da suka jagoranci zanga-zangar hukunci mai tsanani, wanda in taka har ga kisa, kamar dai yadda kafafen yada labaran gwamnatin kasar suka rawaito. Dalilin hakan kuwa shine 'yan adawan sun yi zanga-zangar marawa abin da ya faru a kasashen Tunisiya da Masar baya, ba tare da neman izini daga hukumomin kasar..............
Akalla mutane biyu ne dai suka mutu a taho mugaman da ya faru tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar. Daga cikin wadanda 'yan majalisar dokokin Iran suka nemi a yi musu hukunci mai tsanani sun hada da shugabannin adawa wato Musawi, Karrubi da Chatami, wadanda sune aka zarga da ingiza boren da aka yi, inda magoya bayansu suka ce suma so suke a kara ba su damar walwala da kuma inganta dimokradiyya. Tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi shekaru biyu baya, aka fara fito na fito da gwamnati. To amma wannan barazanar aiwatar da hukuncin kisa, wani abune da zai sa matasa su yi shakkar shiga zanga-zanga, inji wannan mai fafitika 'yar kasar ta Iran.
"Ina ganin wannan zanga-zangar da aka yi, ta tada 'yan adawa dake barci, domin barazanar hukunci mai tsanani da aka nemi a aiwatar kan shugabannin adawa, wani abun tada hankali ne, duk da cewa ban yi tsammanin za a aiwatar musu da hukunci ba. Domin idan hakan ta faru, to lamarin ba zai yi wa shugabannin dadi ba"
Tsarin da gwamnatin Iran ke amfani da shi da kuma zaman doya da manja da kasar ke yi da kasashen yammaci, shine ya sa wannan boren da aka yi jiya har yanzu yake daukar hankalin kafafen yada labarai. Mehram Barati wani masani kan kasar Iran ne dake zama a birnin Berlin, yace wannan zanga-zangar za a yi ta samun irinta, har sai an aiwatar sauye-sauye a gwamnatin kasar.
Wannan zanga-zangar ba za a daina yin ta ba, 'yan kasar Iran sun jira har shekaru 30, yanzu lokacin kawo sauyi yazo. Abin da ya sa hanakan 'yan kasar suna son samun yancinsu, don haka idan gwamnati ta hana su yancin, to zanga-zangar za ta ci gaba. A yar tambaya ita ce, shin a tsawon wata daya ko biyu ko shida ko kuma makwanni biyu za dauka anayi, shine babu wanda zai iya hasace"
Yanzu dai zanga-zanga a kasashen Gabas ta Tsakiya abu ne da ya kasance ruwan dare gama duniya, inda dama yankin ya kasance mafi koma baya wajen mulkin dimokradiyya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu