EU: Ta hori membobinta da su karbi 'yan gudun hijira
August 21, 2021Da take tsokaci game da batun a yayin ziyarar da ta kai a wani sansanin tarbar 'yan gudun hijirar Afghanistan a Spain, shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen, ta ce kungiyar na shirin duba yiwuwar taimakawa kasashe membobinta da suka dauki wani bangare na masu neman mafakar daga Afghanistan.
Sai dai wannan lamarin na zuwa ne a yayin da kawo yanzu kasashen na nahiyar Turai ba su fito fili suka ambaci adadin kaso na 'yan gudun hijirar da suke iya ba wa mafakar ba.
Game da batun ko akwai yiwuwar tuntubar juna tsakanin EU da kungiyar Taliban, Mr von der Leyen cewa ta yi "Akwai abu biyu da nake tsamanin na da muhimmanci shi ne na farko tattaunawa da 'yan Taliban a lokakcin da ake tsaka da matsalar, burinmu shi ne na ganin yadda za mu taimaki jama'a su isa a hilin jirgin saman Kabul, don haka a kwai bukatar tattaunawa da su don ceton rayukan al'umma, amma hakan na da banbanci da tattaunawa ta siyasa domin ba wata tattaunawa irin wannan da Taliban ko kuma ma amincewa da ita."