Shirin bikin Ista a yanayin annoba
April 10, 2020Miliyoyin mabiya addinin Kirista a duniya na a wannan Juma'a shirye-shiryen gudanar da bikin Ista a karshen mako a cikin yanayin annobar cutar Covid 19 a wacce kawo yanzu ta halaka mutane kusan dubu 100 a duniya.
Sai dai bikin istan na bana zai kasance ba armashi a wurare da garuruwa masu tsarki inda mabiya addinin Kiristan suka saba taruwa kamar dandalin Saint-Pierre na birnin Roma inda sai ta hanyar majigi da kuma talabijin ne mabiya za su kalli da kuma sauraren hudubar bikin Istan wanda Paparoma Farancis zai gabatar.
A birnin Jeruzalem a karon farko a cikin sama da karni daya, mujami'ar Saint-Sepulcre da ke zama wajen da mabiya addinin na Kirista ke ayyanawa a matsayin wajen da aka aje gawar Annabi Isa bayan kashe shi, inda kuma ya taso, za ta kasance a rufe.
A kasar Bosniya ma cocin Medjugorje inda mahaifiyar Annabi Isa ta taba bayyana, cocin da ga al'ada ke kasancewa makare da mabiya a wanan mako mai tsarki ga Kiristocin, za ta kasance a rufe a wannan karo a bisa dalillin annnobar Coronavirus.