Shirin ceto kudin Euro ya shiga halin rashin tabbas
September 10, 2012Talla
Peter Gauweiler ya shigar da karar gaggauwa a kotun da ke da mazauninta a birnin Karlsruhe game da halin rashin tabbas da za a fuskanta a dangane da haka Gauweiler ya ce wannan karar martani ne ga shawarar da babban bankin Turai ya tsayar ta rashin kayyade takardun basukan da zai saya daga kasashen Turai da ke fama da bashi. Dan majalisar ya ce yin hakan zai haifar da rudani wajen tsai da hukunci akan shirin ceto kudin Euro, zai kuma yi lahanin gaske ga kasafin kudin Jamus. Ya ce bankin na bukatar janye shirinsa na sayen takardun basukan.
Mawalafiya; Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala