1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Ebadi ta samun kyautar yabo na Birnin Bonn

May 21, 2010

Ebadi wadda ta taɓa samun kyautar yabo ta Nobel akan zaman lafiya yanzu haka tana gudun hijirah domin gujewa hukumomin Iran

https://p.dw.com/p/NTWy
Shirin Ebadi mai fafutukan kare haƙƙin bil'adama na IranHoto: AP

Hukumomin Birnin Bonn a nan Jamus sun baiwa mai fafutukar kare haƙƙin bil'adaman nan kuma lauya 'yar ƙasar Iran Shirin Ebadi kyautar yabo na Kare demokiraɗiyya na ƙasa da ƙasa.

Masu bada kyautar sun yaba da ƙoƙarin da Ebadi keyi na kare haƙƙin bil'adama da kuma demokiraɗɗiyya a Iran.

Ebadi wadda ta taɓa samun kyautar yabo ta Nobel akan zaman lafiya yanzu haka tana gudun hijirah domin gujewa hukumomin Iran.

Ƙasar Iran dai tasha suka daga ƙasshen duniya daban-daban don gane da matakan data ɗauka akan masu fafutukan kare demokiraɗiyya da 'yancin bil'ada.

Yanzu haka kuma akwai ɗaruruwan 'yan adawan ƙasar dake fuskantar shari'a bisa nuna adawa da zaɓen shugaban ƙasa na bara. Ko'a makon nan saida Iran ta zargi wasu Amirkawa uku 'yan yawon buɗe idanu da leƙen asiri.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi