Shirin fitar da sakamakon faduwar jirgin Malesiya
October 13, 2015Talla
Sai dai ana gani bisa duk alamu bayar da wannan sakamako, na iya janyo wani sabon cece-kuce tsakanin kasashen Yamma da Rasha kamar yadda aka fuskanta a baya. Tuni kasar ta Rasha ta kasance cikin shirin kalubalentar wannan sakamako idan har ya kai ga sanyata cikin zargi kamar yadda aka sha cece-kucen a baya. Ofishin kula da harkokin tsaro na kasar Holland (OVV) ne dai aka damka wa alhakin gudanar da wannan bincike.
A ranar 17 ga watan Yuli na 2014 jirgin sama da ya tashi daga birnin Amsterdam bisa hanyar zuwa birnin Kuala Lumpur na Malesiya, ya fado tare da hallaka mutane 298, wanda hukumomin kasar Ukraine suka dora alhakin faduwar jirgin a kan 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha.