1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kara kujerun majalisar dokokin Nijar

April 28, 2014

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar kara yawan 'yan majalisar dokokin kasar daga 113 zuwa 171, karkashin wani kudirin doka da ta sanyawa hannu.

https://p.dw.com/p/1BqQr
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

Gwamnatin Nijar din dai ta kafa hujjarta ta neman kara yawan 'yan
majalisar dokokin da yawan karuwar alummar kasar da aka samu daga shekara ta 2002 zuwa ta 2013 inda sakamakon kidayar al'ummar kasar wanda hukumar kididdiga ta kasa ta bayyan yau da makonni biyu ya nunar da cewa yawan yan kasar ya zarta mutun miliyon 17.

Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou IssoufouHoto: N. Colombant

Su ma dai wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Nijar din irin su Mahaman Sani Amadu na jamiyyar ANDP Zaman Lahiya nuna goyon bayansu suka yi inda Mahaman din ke cewa matakin abu ne da ya dace duba da halin ake ciki a Majalisar.

To ai dai a ganin Saleh Hasan, dan majalisa daga jam'iyyar Moden Lumana Afrika ta bangaren adawa cewa ya yi a ba sa adawa da shirin amma kuma abun na bukatar dogon nazari kafin aiwatar da shi domin kada a yi kitso da kwarkwata.

Su kuwa kungiyoyin fararen hula da ke kasar adawarsu suka nuna da shirin inda guda daga cikins wato Malam Nuhu Arzika ke ganin duk da cewar shirin bai sabawa kundin tsarin mulki ba, amma daukar wannan mataki a yanzu bai dace ba idan aka yi laakari da bukatocin 'yan niger da ma raunin tattalin arzikin da kasar ta ke fuskanta.

Nan gaba ne gwamnatin kasar za ta aika da wannan kudirin doka ga majalisar dokokin Nijar din don tafka muhawara kansa kafin su yanke hukunci.

Sitzung der Nationalversammlung in Niamey Niger
'Yan majalisar dokokin Nijar yayin wani zama a zauren majalisarHoto: DW

Mawallafi: Gazali Abdou Tassawa
Edita: Pinado Abdu-Waba